Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta kama wani dan kasuwa mai suna Emmanuel Okechuku Orjinze dan shekaru 48 a duniya, dan asalin kasar Faransa, bisa zarginsa da hadiye sunkin hodar iblis 111.
Ya amayar da haramtattun kwayoyin ne bayan kwashe kwanaki a hannun NDLEA bayan kama shi a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe, Abuja.
- NDLEA Ta Kama Wani Fasinja Ɗauke Da Kwayar Tramadol 4,000 A Filin Jirgin Sama Na Legas
- NDLEA Ta Kona Kilo 304,436 Tare Da Lita 40,042 Na Haramtattun Kwayoyi Da Aka Kama A Legas Da Ogun
Okechukwu wanda ya yi ikirarin cewa shi kwararren dan wasan kwallon kafa ne a nahiyar Turai, an kama shi ne a ranar Talata 21 ga watan Mayu, yayin da ake binciken jirgin Airfrance mai lamba AF 878 daga Abuja zuwa birnin Paris na kasar Faransa.
Binciken na’u’ra ya tabbatar da cewa, wanda ake zargin ya hadiye haramtattun kwayoyin ne bayan an tsare shi a hannun hukumar inda ya a mayo jimillar hodar iblis 111 masu nauyin kilogiram 1.603 cikin kwanaki uku.