Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya kaddamar da rabon kayayyakin noman rani na hukumar raya arewa maso gabas (NEDC) ga manoma a kananan hukumomi 17 da ke jihar.
Buni, wanda ya samu wakilcin mataimakin gwamna, Hon. Idi Barde Gubana, ya ce, “Hukumar NEDC ta dade tana tallafawa jihar Yobe inda yanzu haka, ta kara tallafawa manoman yankin.”
- Gwamnatin Katsina Za Ta Ciyar Da Marasa Karfi Mutum Fiye Da Miliyan 2.1 A Ramadan
- Tsadar Rayuwa: Gwamna Yusuf Ya Roki Tinubu Ya Sake Bude Iyakokin Nijeriya
Ya kara da cewa, tallafin ga manoman yazo a daidai lokacin da ake da mutukar bukatar hakan, wanda zai inganta samar da abinci a jihar.
Gwamnan, ya bukaci wadanda suka ci gajiyar shirin da su yi amfani da kayan aikin noman yadda ya kamata domin amfanin al’ummarsu da ma jihar baki daya.