Gwamnatin tarayya ta hannun hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa, NEMA a ranar Lahadin nan ta fara rabon kayan agaji ga wadanda ambaliyar ruwa ta 2022 ta shafa a jihar Kwara.
Gwamnan jihar, AbdulRahaman AbdulRazaq, ne ya kaddamar da rabon kayayyakin tallafin, wanda mataimakinsa Mista Kayode Alabi ya wakilta.
- An Bizne Gawar Jakadan Nijeriya Na Kasar Faransa A Jihar Kwara
- An Maka Sarkin Ilorin A Kotu Kan Hana Bikin Gargajiya A Kwara
Wadanda suka ci gajiyar rabon wadanda suka fito daga kananan hukumomi 12 a jihar, sun hada da manoma da masu karamin karfi.
Kayayyakin da aka raba wa wadanda suka ci gajiyar tallafin sun hada da kayayyakin noma, kayan abinci, keken dinki, injin nika da katifu.
A nasa jawabin, babban daraktan hukumar NEMA, Mustapha Ahmed, wanda ya samu wakilcin Mista Ephraim Tony, shugaban sa ido da tantancewa a hukumar, ya ce gwamnatin tarayya ta amince da daukar matakin ne musamman ga mutanen da ambaliyar ruwa ta 2022 ta shafa.