Tawagar Super Eagles ta Nijeriya ta fara sauran wasannin share fagen shiga gasar Kofin Duniya ta shekarar 2026 da kafar dama bayan ta lallasa ƙasar Gabon da ci 4 da 1 a wasan da suka buga a filin wasan Moulay Hassan da ke birnin Rabat na ƙasar Maroko.
Wasan wanda aka fara da misalin ƙarfe 5 na yamma agogon Nijeriya ya ɗauki hankalin dubban masu sha’awar ƙwallon ƙafa a Nahiyar Afirika, duba da cewa duka ƙasashen biyu babu kanwar lasa a cikinsu.
- An Gudanar Da Taro Mai Taken “Shugabancin Duniya: Ayyukan Matasa” A Johannesburg Dake Afirka Ta Kudu
- NDLEA Ta Ƙona Miyagun Ƙwayoyi Sama Da Kilo 52,000 A Kaduna
Akor Adams da ke buga ƙwallo a ƙungiyar ƙwallon kafa ta Sevilla ne ya fara jefa ƙwallo a ragar Gabon a minti na 78 kafin Mario ya farke ƙwallon a minti na 90 na wasan wanda hakan ya janyo aka tafi ƙarin mintuna 30 domin ganin wanda zai yi nasara.
A minti na tara cikin ƙarin lokaci ne Ejuke ya zura ƙwallo ta biyu a ragar Gabon, kafin Victor Osimhen ya zura ƙwallaye biyu a sauran mintunan ƙarshe na wasan.
Nijeriya za ta haɗu da ƙasar Kamaru ko Dimokuraɗiyyar Kongo a wasa na gaba.













