Newcastle United ta sayi dan wasan Ingila Harvey Barnes daga Leicester City kan kudi kusan fan miliyan 38.
Dan wasan mai shekaru 25, wanda ya bugawa Ingila wasa sau daya, ya sanya hannu kan kwantiragin shekaru biyar da Magpies
Shi ne dan wasa na uku da kungiyar ta siya a bazara bayan zuwan dan wasan gaba Yankuba Minteh da dan wasan tsakiyar kasar Italiya Sandro Tonali
Na ji dadin zuwa nan domin kulob ne mai ban mamaki kuma a gare ni babbar dama ce ta zo in shiga cikin tawagar da ta yi nasara
Kuma wadda da ke yin abubuwa masu ban sha’awa, don haka ina matukar sha’awar kasancewa a nan
Newcastle ta kare a matsayi na hudu a gasar Premier kakar bara, kuma a shekarar 2023-24 za ta buga gasar zakarun Turai a karon farko tun 2003-04
Kocin Newcastle Eddie Howe ya ce “Harvey gwani ne mai ban sha’awa wanda na dade ina sha’awar shi don haka ina farin cikin maraba da shi zuwa Newcastle United
Yana da karfi, mai sauri kuma yana da kyau a tsakiya kuma ya nuna a kakar wasa ta bara musamman cewa yana da ido don cin kwallo
Barnes shine dan wasa na baya bayan nan da ya bar Foxes bayan faduwa daga gasar Premier
Ya buga wa Leicester wasanni 146 na gasar Premier, inda ya zura kwallaye 35 ya kuma taimaka aka zura kwallaye 25
Duk da zura kwallaye 13 a gasar 2022-23, bai iya ceton su daga faduwa a gasar Premier ba
Tafiyar nasa na zuwa ne bayan James Maddison ya koma Tottenham a kan kudi fam miliyan 40, yayin da takwaransa na tsakiya Youri Tielemans da mai tsaron baya Caglar Soyuncu suka fice daga kungiyar kyauta, inda suka koma Aston Villa da Atletico Madrid