Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German, Neymar, ya zura kwallaye 200 a raga a kungiyoyin da ya bugawa wasa tun daga lokacin da ya fara buga kwallo a kwallon kafa a duniya.
A ranar Lahadin ata gabata Paris St Germain ta yi nasara a kan Olympic Marseille da ci 1-0 a wasan mako na 11 a gasar Ligue 1 kuma Neymar ne ya ci kwallon da ya bai wa PSG maki ukun da take bukata a karawar da suka yi a wasan hamayya a Parc des Princes.
Dan wasan Brazil, ya ci kwallon a minti na 45 kuma ta 200 tun daga Santos da Barcelona da kuma Paris St-Germain sai dai Lionel Messi ya buga wasan ya kuma samu dama biyu ta cin kwallo, sai dai mai tsaron raga Pau Lopez ya nuna kwazonsa.
Marseille ta karasa gumurzun da ‘yan wasa 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Samuel Gigot jan kati, sakamakon ketar da ya yi wa Neymar kuma Marseille ta samu damar cin kwallo ta hannun Jonathan Clauss, amma Gianluigi Donnarumma ya tsare ragar yadda ya kamata.
Da wannan sakamakon PSG, wadda ta ci wasa tara da canjaras biyu a karawa 11 ta ci gaba da jan ragamar teburin Ligue 1 da tazarar maki uku tsakaninta da Lorient ta biyu.