Kabiru Alhassan Rurum, mamba mai wakiltar mazabar Rano, Kibiya, da Bunkure na tarayya, ya yi watsi da dakatarwar da aka yi masa daga jam’iyyar NNPP a Kano.
Da yake mayar da martani kan sanarwar dakatarwar da shugaban NNPP na Kano Hashim Sulaiman Dungurawa ya bayar, Rurum ya jaddada cewa, shi da takwarorinsa ba su taba zama tare da bangaren da suka sauya tambarin jam’iyyar ba, yana mai jaddada cewa, su suna cikin bangaren NNPP mai kayan marmari.
- Da Ɗumi-ɗumi: NNPP Ta Dakatar Da Sanata Kawu Sumaila Da Wasu ‘Yan Majalisa Uku
- Ba Ni Da Sha’awar Sake Shugabantar APC, Gwamna Nake Burin Zama – Abdullahi Abbas
Daiiy Trust ta ruwaito cewa, Rurum da Madakin Gini sun fito fili sun ware kansu daga tafiyar NNPP mai tambarin Alkalami da Littafi tare da bayyana cewa, suna tare da jam’iyyar NNPP mai kayan marmara.
Ya ce, “Duniya ta san tun da suka sauya tambarin jam’iyyar, ba mu tare da su. Muna cikin NNPP mai tambarin kayan marmari su kuma suna mai tambarin Alkalami da littafi.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp