Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakata Abdullàhi Umar Ganduje ya tuna wa duk wani mutum musamman jagoran darikar Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso cewa da zarar sun dawo cikin Jam’iyyar APC, to ko shakka babu ya zama jagoransu.
Ya ce matukar kana dauke da katin kasancewar dan jam’iyyar APC kowane kai, to kana biyayya ne ga shugaban jam’iyya na kasa, haka lamarin yake ga shugabannin mazabu da na jiha da kuma shiyya-shiyya.
- Kiraye-kirayen Maye Ganduje Da Kwankwaso: Dattawan APC Sun Mayar Da Martani
- Ganduje Ya Zargi ‘Yan Siyasa Da Hannu A Haddasa Rikice-rikicen Zabe
Ganduje ya bayyana haka ne ga dandazon magoya bayan jam’iyyar APC a Kano, inda ya bukace magoya bayan da cewa kar su ji wata fargabar wani zai shigo cikin jam’iyyar.
Ya kara da cewa kar ku ji tsoron komai don wani ya zo gidanku domin amfanar wani abu, da ka je gidan wasu neman wani abu, da a zo gidanku neman wanne za ka zaba.?
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp