Hukumar NDLEA ta Nijeriya da takwararta ta Indiya sun amince da yin aiki tare domin daƙile safarar miyagun ƙwayoyi tsakanin ƙasashen biyu. Wannan yarjejeniya ta fito ne daga wata tattaunawa ta kafar intanet tsakanin Shugaban NDLEA na Nijeriya, Janar Buba Marwa (mai ritaya), da shugaban hukumar ta Indiya, Anurag Garg.
Shugabannin sun jaddada buƙatar haɗin gwuiwa, musamman wajen hana shigo da haramtattun magunguna daga Indiya zuwa Nijeriya. Marwa ya ce akwai buƙatar a ƙarfafa wannan dangantaka bisa yarjejeniyar da aka rattaba wa hannu a shekarar 2023.
- Bayan Shekaru 7 Yana Ɓoye, NDLEA Ta Cafke Babban Dillalin Ƙwayoyi
- NDLEA Ta Kai Samame Fitattun Wuraren Shaye-shaye, Ta Cafke Mutane 19 A Kano
Buba Marwa ya roƙi hukumar Indiya da ta tallafa wa NDLEA ta hanyar bai wa jami’anta horo na musamman domin inganta dabarunsu wajen yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi.
Nijeriya na daga cikin ƙasashen da ke fama da matsalar shaye-shaye da safarar miyagun ƙwayoyi, wanda hakan ya sa aka kafa NDLEA domin daƙile wannan barazana ga lafiyar jama’a da zaman lafiya a ƙasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp