Gwamnatin tarayya ta nuna damuwarta kan maƙudan kudaɗen da cutar hanta ke ƙalume ga ƴan Nijeriya, inda ta yi kiyasin cewa ƙasar na yin asarar tsakanin naira tiriliyan 13.3 zuwa naira tiriliyan 17.9 a duk shekara sakamakon cutar.
Ministan lafiya da walwalar jama’a, Farfesa Muhammad Ali Pate, shi ne ya shaida hakan a lokacin da ke ganawa da ƴan jarida yayin bikin tunawa da masu cutar hanta ta duniya na 2025, da ya gudana a Abuja.
Ranar cutar hanta ta 2025, mai taken ‘Hepatitis: Let’s ɗisk It ɗown’, Minista ya yi kira da a dauki matakin gama gari don shawo kan matsalolin kiwon lafiya, tsari, da zamantakewa da ke hana miliyoyin mutane samun kulawa ta yadda za su sarrafa cutar har zuwa ganin sun warke daga cutar ta hanta.
Ministan wanda ya samu wakilcin daraktan kula da lafiyar jama’a, dakta Godwin Ntadom, ya kuma shaida cewar kaso 8.1 cikin 100 na ƴan Nijeriya na dauke da cutar hanta mai mataki ta ‘B’, sannan kuma duk kuwa da wadatar rigakafi da magunan cutar, sama da kaso 90 cikin 100 na wadanda suka kamu da cutar ba su zuwa jinya ko shan magani kuma ko su sani ko ba su sani ba suna sake yada kwayar cutar ga wasu mutanen na daban musamman yara.
Ya ce, “Ana yin kuskuren gano alamomin cutar da ke zuwa da kimannin zazzaɓin cizon sauro, yanayi kamar zazzaɓi, gajiya da rashin lafiya, yawanci ana magance su ta hanyar maganin kai, yayin da kwayar cutar ta yi gum cikin jiki tana lalata hanta kuma tana iya kaiwa ga a kamu ciwon hanta mai tsanani ko kuma ciwon daji.
“Kiyasin ƴan Nijeriya miliyan 20 ke rayuwa da cutar hanta, kuma mutum miliyan 18.2 sun kamu ne da cutar rukunin B, sannan wasu mutum miliyan 2.5 sun kamu da cutar rukunin C. Abin takaici, ƴan Nijeriya 4,252 ne ke mutuwa a duk shekara sakamakon ciwon hanta da aka kasa maganceta ke haifarwa,” ya shaida.
A jawabinsa na fatan alkairi, mai riƙon muƙamin wakilin hukumar kula da lafiya ta duniya (WHO) a Nijeriya, dakta Aleɗ Gasasira, ya yi kira ne ga gwamnatin tarayya da ta tashi tsaye wajen yin na mijin ƙoƙari kan cutar hanta, yana mai cewa cutar tana shafar miliyoyin jama’a a ƙasar nan.
Gasasira, wanda ya samu wakilcin dakta Mya Ngon, a faɗin ofishin WHO da ke Nahiyar Afirka, ya ce sama da mutum miliyan 70 ke rayuwa da cutar hanta rukunin Ba ko C, amma har yanzu kaso 1 a cikin 10 na wadannan masu dauke da cutar ne ke amsar magani ko suka yi maganin cutar.
Wakilin WHO ya jinjina wa Nijeriya bisa ci gaba da aiwatar da shirin daƙile yada cutuka daga cikin uwa zuwa jarirai da suka hada da cutar nan mai ƙarya garkuwa jiki (ƙanjamau), cutar hanta, da STIs.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp