Bayan fara fafutukar yaki da cin zarafin mata na tsawon kwana 16, shugabannin kasashen duniya sun nuna matukar damuwarsu dangane da karuwar annobar a Nijeriya.
Majalisar Dinkin Duniya da Bankin Duniya sun bayyana cewa, Nijeriya na bukatar kusan Naira tiriliyan daya; don magance cin zarafin da ake yi wa mata.
- Yadda Matatar Mai Ta Fatakwal Ta Fara Aiki
- Nijeriya Ta Shirya Magance Matsalar Almajirai – Tinubu Ga Macron
Sun kwatanta kudaden da ake kashewa wajen cin zarafin matan a Nijeriya da kimanin kashi 1.5 cikin 100 (N1.06 trillion) na tattalin arzikin da take samu a kowace shekara.
Shugabannin kasashen duniyar, sun bayyana haka ne a wajen taron kaddamar da ma’aikatar harkokin mata ta 2024, da aka gudanar na tsawon kwana 16; domin fafutukar yaki da cin zarafin mata na wannan shekara a Abuja.
Da take gabatar da jawabi a wajen taron, Daraktar Hukumar Kula da Mata ta Majalisar Dinkin Duniya; Beatrice Eyom ta bayyana cewa, cin zarafin wani bangare na jinsi; wanda ya wuce batun musgunawa mata kadai ko wasu sauran jinsina, domin kuwa yana da tasiri wajen tauye ci gaba da kuma tattalin arzikin kasa.
“Idan muka duba, za mu fahimci cewa; kusan kashi 42 na matan Nijeriya ba masu kudi ba ne; idan muka kwatanta su da kashi 35 cikin 100 na maza, musamman idan kuma muka yi la’akari da matan da ke rike da mukamai a kasar kashi 5 ne kacal na wadanda aka zaba. Haka nan, Nijeriya ta fuskanci mummunar asara a bangaren tattalin arziki; wanda aka kiyasta cewa ya kai kimanin kashi 1.5 na kudaden da take samu a duk shekara, inda hakan ke kawo cikas ga ci gaban kasar.
“Wannan rikici na jinsi, ya wuce batun miji ya doki matarsa kadai. Abu ne wanda zai iya rage ci gaban tattalin arzikin kasa. Don haka, ba za ta taba rabuwa da talauci ba; muddun ba a rage ko kawo karshen cin zarafin da ake yi wa mata ba”, in ji Eyom.
Da yake kiyasta asarar da Nijeriya ta yi ta fuskar tattalin arziki (Kashi 1.5 cikin 100) da ke da alaka da cin zarafin mata, tiriliyoyin Nairori ne a kowace shekara, Daraktan Bankin Duniya a Nijeriya; Mista Ndiamé Diop ya yi nuni da cewa, ba a yi la’akari da alkaluman da aka yi asara na sa’o’in aiki da kasuwancin da aka dakile jinsin matan ba.
“Tasirin cin zarafin matan ta fuskar tattalin arziki, na da matukar yawa. Kudaden da gwamnatin tarayya ke warewa don yaki da cin zarafin matan; ana karkatar da su ne wajen kula da lafiyar yara ko wasu nau’o’in kalubaben matsalar kiwon lafiya a kasar,” in ji Diop wanda wani jami’in Bankin Duniya ya wakilta a wurin taron.
Da yake mayar da martani game da koma bayan da ake samu a bangaren kudi, don magance matsalar cin zarafin ‘ya’ya mata da kuma kiran Eyom ga gwamnati da ta zuba hannun jari wajen aiwatar da manufofin jinsi, adalci da kuma hana cin zarafin mata, Diop ya ce; Bankin Duniya ya himmatu wajen ganin ya taimaka wa gwamnatin Nijeriya, domin yaki da wannan cin zarafi na mata.
“A cikin kudaden da suke ajiye a banki, kimanin dala biliyan 17; an ware dala biliyan 540, domin karfafa tattalin arzikin mata. A matsayinmu na banki, mun himmatu wajen tallafa wa Nijeriya tare kuma da inganta tattalin arzikin mata.
Har ila yau, mun mayar da hankali wajen kamfen din yaki da cin zarafin matan ta hanyar tanadar kimanin kusan dala biliyan 17, domin aiwatar da wannan kudiri”, in ji Diop.
Rahoton da LEADERSHIP ta bayar, bugu na 2024 na kamfen din shekara-shekara, mai taken ‘Towards Beijing +30: Hada kai don kawo karshen cin zarafi ga mata’, ya yi kira ga daidaikun mutane da kungiyoyin mata da kuma sauran kungiyoyi, da su yi kokarin daukar matakan kawar da cin zarafi ta hanyoyin da aka tsara kamfen din kowace rana.
A nata bangaren, Babbar Daraktar Cibiyar Sadarwa da Zamantakewar Al’umma; Madam Babafunke Fagbemi, ta bayyana matukar damuwarta; kan yadda ake ci gaba da samun karuwar cin zarafin matan a duniya.
Madam Fagbemi, a wata sanarwa da ta fitar a Abuja ta ce; alkaluman baya-bayan nan da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar kan wannan lamari, ba kawai abin tayar da hankali ba ne; abu ne da ya kyautu a ce kowa ya farka daga barcin da yake yi tare da bayar da gudunmawa wajen kawo karshen wannan cin zarafi da ake yi wa wadannan mata da kuma sauran ‘yan mata.
Dangane da sabon rahoton Majalisar Dinkin Duniya, Ofishin Majalisar Dinkin Duniyar kan hana shan miyagun kwayoyi da aikata laifuka (UNODC) da aka yi wa lakabi da ‘Kisan da maza ke yi wa mata da ‘yan mata a 2023: Kididdigar da aka aiwatar a duniya ta tabbatar da cewa, a kullum ta Allah ana kashe mace ko budurwa a duk minti 10; ko dai miji ya kashe matar ko saurayi ya kashe budurwarsa ko kuma danginsu su yi kisan.
A 2023 kadai, mata da ‘yan mata kimanin 85,000 aka kashe da gangan a duniya, sannan kashi 60 cikin 100 na wadanda aka kashe din ma’ana kimanin su 51,000, sun mutu ne sanadiyyar mazajensu ko kuma dangin mazajen nasu.
Rahoton ya sake bayyana cewa, Afirka ce a gaba wajen samun yawan wadanda ke aikata wannan kisa a tsakanin ma’aurata da danginsu a 2023, sai kuma Kasar Amurka da sauran kasashe kamar irin su Australiya da sauran makamantansu. A Turai da Amurka kuma, yawancin matan da aka kashe a cikin gida; kashi 64 da kuma 58 cikin 100; mazajensu ne suka kashe su. Haka nan, a wasu yankunan kuma; dangin mazajen ne ke da hannu wajen aikata kisan.
Ko shakka babu, wadannan alkaluma sun nuna yadda ake cin zarafin mata da ‘yan mata, wanda kuma akwai bukatar hada hannu wuri guda; domin daukar tsauraran matakai.