Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya ce Nijeriya na fuskantar kalubale amma akwai yadda za a yi a shawo kansa, kasancewar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu mutum ne da ke cike da kishi da basira da kuma iya tafiyar da al’ummar kasar kan turbar ci gaba.
Ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a lokacin da ya karbi bakuncin ministan raya kasa na kasar Denmark, Mista Dan Jorgensen, a wata ziyarar ban girma da ya kai fadar shugaban kasa a Villa, Abuja.
- Kungiyar Kwadago Ta Tsunduma Yajin Aiki Yau Talata
- Nuhu Ribadu Ya Yaba Wa Sojoji Kan Nasarar Da Ake Samu A Yaki Da Ta’addanci
Mataimakin shugaban kasar ya ce, Nijeriya na da babbar dama a fannin fasahar zamani (dijital), masana’antu da kuma bangaren makamashi, don haka, kasar na karfafa masu zuba jari acikin shirinta na habaka tattalin arziki.
Tun da farko, Ministan na kasar Denmark, Jorgensen, ya bayyana jin dadinsa ga jagorancin Nijeriya da jajircewarta wurin dorewar yanayi.