Gwamnatin tarayya ta ce, ta himmatu wajen bunkasa zirga-zirga da furin jiragen sama ta hanyar amfani da dabarbarun fasahar tattaron dan adam.
Ministan kula da jiragen sama a Nijeriya, Mista Festus Keyamo, shi ne ya shaida hakan a lokacin da ke bude taron kwamitin kula da tauraron dan adam na tekun Indiya (AFI) da ya gudana a Abuja ranar Litinin din da ta gabata.
- An Samu Sabuwar Damar Kyautata Hulda Tsakanin Sin Da Hungary
- Shekaru 14 Bayan Rasuwar Yar’Adua: Wasu Nasarori Da Ya Cimma A Rayuwarsa
A cewar Keyamo, fasahar tauraron dan adam zai mafita wajen ganin an bunkasa bangaren sufurin jirage, tun daga tsarin bunkasa kula da sufurin jiragen sama zuwa, bunkasa iya hasashen yanayi cikin sauri da sauki.
“Ta hanyar amfani da wadannan damarmakin, za mu iya habaka kula, inganta aiki, da bude kofofin bunkasa damarmaki. Ina tsaye a gabanku domin jinjina muku kan kokarinku wajen kyautata sauya fasahar tauraron dan adam.
“A kasashen da suka ci gaba, ana amfani da tauraron dan adam wajen tafiya da harkokin sufuri sosai, wajen bada damar kula da lafiya, da daurewar zirga-zirga.
“Gwamnatin tarayya ta himmatu wajen ganin ta kyautata rayuwar jama’a ta hanyar kyautata tattalin arzikinsu da kuma tabbatar da tsaronsu, gwamnati ba ta wasa da tsaron jama’anta ta kowani bangare.
“Don haka dukkanin hanyoyin da suka dace mu bi wajen kyautata tsaro ta hanyar sufuri za mu bi, shi ya sa muka dukufa wajen rungumar fasahar tauraron dan adam wajen kyautatawa da saukaka sufuri,” ya shaida.