Gwamnatin tarayyar Nijeriya da Kasar Saudiyya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar gudanar da aikin hajjin 2024 a Jedda.
Ministan harkokin waje, Yusuf Tuggar shi ne ya jagoranci tawagar Nijeriya, yayin da ministan gudanar da aikin Hajji da Umara, Dakta Taufik Al-Rabiah ya jagoranci tawagar Saudiyya.
- Shari’ar Kano: Kanawa Na Farin Ciki Kan Nasarar Abba A Kotun Koli
- Shiriya, Ni’ima Da Gaskiyar Manzon Allah (SAW)
Mataimakiyar daraktan harkokin hukumar aikin hajjin Nijeriya, (NAHCON), Fatima Usara ta bayyana cewa tawagar ‘yan Nijeriya da suka halarci taron rattaba hannun ciki har da mukaddashin shugaban hukumar NAHCON, Jalal Arabi, sun bukaci karin wa’adi ga masu jigilar ‘yan Nijeriya tare da neman a kawo karshen matsalar da aka samu a lokacin hajjin bara a Mina.
Haka kuma gwamnatin tarayya ta bukaci ministan aikin hajji da umara na Kasar Saudiyya da ya ziyarci Nijeriya.
A nasa bangaren, Rabiah ya amince da kalubalen da aka samu a aikin hajjin bara a Mina, sannan ya bayar da tabbacin cewa ana kokarin inganta amfani da murabba’in fili mita miliyan 2 ga maniyyata miliyan biyu domin gudanar da aikin hajj a duk shekara.
Da yake amsa goron gayyatan zuwa Nijeriya nan ba da jimawa ba, Rabiah ya bayyana goyon bayan ma’aikatar wajen daukar matakan da suka dace na bai wa alhazai yanayi mai kyau domin gudanar da aikin hajji cikin natsuwa.
Haka kuma ya jaddada wa tawagar hukumar NAHCON sabon tsarin da aka fito da shi a harabar Masha’ir.
Dangane da bukatar da NAHCON ta shigar na samar da isasshen fili a Mina, Rabiah ya bayyana muhimmancin ajiye kudade da wuri domin samun wuraren da ya dace a Masha’ar, inda ya ce hakan ya sa ma’aikatarsa ta sabunta tsarin wanda ya riga zuwa shi za a fara la’akari da shi.
Ya bukaci NAHCON ta yi kokarin cin gajiyar wannan sabon tsari domin samun wuri a Masha’ir, kamar Kasar Saudiyya take kokarin guda da adalci wajen samun wuri.