Gwamnatin tarayya ta nuna damuwarta kan cewa kasar nan ta yi asarar tiriliyoyin naira sakamakon ayyukan masu hakar ma’adanai ta barauniyar hanyoyi musamman a jihohi.
Gwamnatin ta kuma cafke da gurfanar da ‘yan kasan waje su hudu wadanda suka shiga harkar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, yayin da wasu mutane 320 kuma aka cafke kan harkokin satar ma’adinai.
- Yadda Fadada Bude Kofar Kasar Sin Ke Haifar Da Damammaki Ga Duniya
- Xi Jinping Ya Halarci Bitar Tawagar Lardin Jiangsu
A cewar gwamnatin, cikin wadanda aka kama 320, kusan mutum 150 a halin yanzu suna fuskantar shari’a kuma wasu guda tara an dauresu, inda su kuma mutum hudu ‘yan kasar wajen aka dauresu a gidan yari.
Ministan bunkasa albarkatun kasa, Dele Alake, shi ne ya shaida hakan a lokacin da ke ganawa da manema labarai a karshen zaman majalisar zartarwa na tarayya (FEC) wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jagoranta.
Ministan ya kuma ce, gwamnatin tarayya ta fuskanci kalubale wajen shawo kan matsalar hako zinari, musamman a arewacin Nijeriya, saboda al’adu.
Alake ya bayyana cewa majalisar zartarwar ta amince da wani sabon shiri na inganta tsari da kuma dakile asarar kudaden shiga a fannin ma’adinai.
A wani bangare na shirin, ya ce gwamnati za ta tura fasahar tauraron Dan’adam don sa ido kan muhimman wuraren hakar ma’adinai da kuma bin diddigin ayyukan ma’adani.
Alake ya kara da cewa gwamnatin tarayya za ta karfafa aikin hadin gwiwa a tsakaninta da gwamnatin jihohi a yankunan da ake hakar ma’adinai domin dakile ayyukan masu haka ba bisa ka’ida ba, domin tabbatar da cewa kasar na morar albartun da Allah ya huwace mata.
Da yake magana kan takardar da ya gabatar a gaban majalisar, ministan ya ce takardar ta tsara yadda za a shawo kan masu hakar ma’adinai ba tare da lasisi ba da gudanarwa ba bisa ka’ida ba, lamarin da ke janyo nakasu sosai ga kudaden shiga a kasar nan.
A cewarsa, muddin aka fara amfani da sabon tsarin, kasar nan za ta samu damar bibiya da kallon yadda ake gudanar da lamarin, sannan za a samu damar gano wadanda suke karkatar da albarkatun kasar domin dakile satar ma’adinai.
Ministan ya ce kwanan nan kuma za a fara amfani da tauraron Dan’adam wajen bibiyar ayyukan hakar ma’adinai, wanda ya ce al’umma za su ga tasirinsa matuka gaya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp