Hukumar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa NPA, ta sanar da cewa, Nijeriya ta zama daya daga cikin mambobi a kungiyar Tashoshin Jiragen Ruwa Ta kasa da kasa IPCSA.
Shugaban Hukumar, Dakta Abubakar dantsoho ya bayyana haka a jawabinsa taron aikin bunkasa kasuwanci na kasa wato NSW wanda aka tattaunawa da masu ruwa da tsaki da ya gudana a jihar Legas.
Ya sanar da cewa, an amince da Nijeirya shiga cikin kungiyar ne, bayan a cika dukkanin sharuddan da suka kamata.
- Yadda Safarar Bakin-haure Ke s Ta’azzara A Afirka -Bincike
- Kamfanin Harhaɗa Mota Na Dangote Ya Kera Peugeot 3008 GT A Kaduna
Da yake yin bayani kan mahimmancin aikin NSW, dantsoho ya bayyana cewa, Hukumar ta NPA, ta samar da wasu ka’idoji da za su taimaka wajen kara ciyar da Hukumar gaba.
“Shigar Nijeriya cikin kungiyar, ya bata damar kai wa wani mataki na manyan Tashoshin Jiragen Ruwa da ke a yankin kamar irin na kasashen Morocco, Ghana, Togo, Ibory Coast, da jamhuriyar Benin, da sauransu”. Inji dantsoho
Shugaban ya sanar da cewa, shigar Hukumar cikin kungiyar, zai magance kalubalen jinkiri cunkoson da ake samu tare da kuma samar da hadin kai a tsanin matakan gwamnati da kuma tafiyar da ka’idojin da aka gindaya.
“Yarjeniyar wacce aka rattaba hannu a kanta a watan Afirilun 2019, ta zama wajbi da Jiragen Ruwa da Tashoshin Jiregen Ruwa, tabbatar da cewa, sun karfafa ta a karkashin aikin na NSW, A 2024”. A cewwar dantsoho.
dantsoho ya kara da cewa, duba da mahiimancin na NSW, NPA ta tsara tare da kuma wanzar da na ta, dabarun a karkashin shugabancinta.
Ya ce, NPA ta dauki kwararn matakai na rungumar tsarin kimiyyar ICT, mussamman domin ta wanzar da jerin ayyukanta, a cikin gida.
dantsoho ya jaddada cewa, aikin na NSW wanda ke a karkashin kulawar Ministan hada-hadar bunkasa kasuwancin teku Adegboyega Oyetola, an mayar da hankali wajen ganin an wanzar da shi.