Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Nijeriya,(NFF), Ibrahim Gusau, yana bayyana kwarin gwiwar cewa tawagar kwallon kafa ta Nijeriya,(Super Eagles) za ta samu gurbin shiga gasar cin kofin duniya na FIFA na shekarar 2026, Super Eagles ba ta samu damar shiga gasar ba kai tsaye amma tana da wata dama ta hanyar wasannin share fagen shiga gasar.
Tawagar wadda Eric Chelle ke jagoranta za ta fafata da takwararta ta kasar Gabon (Gabonese Panthers) a wasan kusa da na karshe na wasannin share fagen shiga gasar a filin wasa na Prince Héritier Moulay El Hassan da ke Rabat babban birnin kasar Moroko da yammacin yau Alhamis.
Idan suka yi nasara a wasan, za su hadu da ko dai Indomitable Lions na kasar Cameroon ko Leopards na jamhuriyar tarayyar Congo a wasan karshe, Gusau ya bayyana cewa Super Eagles suna da kwarewar samun nasara a wasannin da zasu fafata a Moroko, “zamuyi nasara idan muka yi abin da ya dace,” in ji shi.
“Mun yi imani cewa ‘yan wasanmu tare da kwarewar da suke da ita, zai janyo wa Nijeriya abin alfahari, ba kawai a ranar Alhamis ba, har ma a duk tsawon wasannin share fagen da zamu buga”, hakan yasa muke da kwarin gwuiwar cewar kasarmu za ta iya samun tikitin shiga gasar cin kofin Duniya,” in ji Gusau.














