Hukumar Kula da Harkokin Tsaron Tashoshi Jiragen Ruwa ta Kasa (NIMASA) ta bayyana cewa, dakatar da kudaden da kamfanonin da ke ketare ke cazar kan Jiragen ruwan da suka yo dakon kaya daga waje da ake shigowa da su zuwa cikin kasar nan, hakan zai adanawa Nijeriya dala biliyan 400, a duk shekara.
Jami’in sashen hudda da jama’a na Hukumar Osagie Edward, ya bayyana haka a cikin sanarwar da ya fitar.
- Trump Ya Dakatar da Harajin Da Sanya Wa Ƙasashen Duniya, Ya Ƙi Cire Wa China
- USAID Za Ta Dawo Aiki A Wasu Ƙasashen Duniya – Gwamnatin Amurka
Osagie ya bayyana cewa, asali an dorawa Nijeriya nauyin biyan wannan kudaden ne, a lokacin da ayukan ta’asar tsagerun Nija Delta da kuma na ‘yan fashin teku.
Ya kara da cewa, koda yake dai, Hukumar Kiddiga ta Kasa NBS, bata da wasu alkaluma na yawan jimmlar kudaden da aka biya cazar kan Jiragen ruwan da suka yo dakon kaya daga waje da ake shigowa da su zuwa cikin kasar nan.
Ya ci gaba da cewa, amma wasu alkaluma sun nuna cewa, a cikin shekaru uku kacal da suka gaata, Nijeriya, ta biya sama da dala biliyan 1.5 na wadannan kudaden ga kamfanin Lloyd da ke a kasar Birtaniya.
A cewarsa, wadannan kudaden sun hada da biyan kudaden samar da kariya da na inshore da kuma sauran kudaden da ake biyan kamfanonin na waje.
Ya sanar da cewa, wadanan kudaden da ake biya, na shafar ci gaban tattalun arzikin kasar, inda ya yi nuni da cewa, duk Jirgin ruwa daya da ya yi dakon Danyen Mai ana biyan dala miliyan 130, inda kuma ake cazar kudin da suka kai akalla dala 445,000.
Kazalika, Osagie ya bayyana cewa, ana jigilar Kwantaina kuma ana biyan dala miliyan $150, wanda kuma ake cazar dala 525,000, kan kowacce jigila daya.
Kamfanin Maersk, daya daga cikin manyan kamfanoni a duniya da ke dakon kaya, ya kirkiro kowacce Kwantaina na biyan dala 450, wanda kuma yake cazar daga dala 40 zuwa dala 50 a kan Kwantaina 20.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp