Cibiyar Masu Binciken Adadi ta Nijeriya (NIQS) ta yi kira ga gwamnatin tarayya da Majalisar Dokoki ta Kasa da su samar da mafita wajen kayyade kudin hayar gidaje, musamman a manyan birane, kamar Abuja.
Shugaban Cibiyar, QS Kene Nzekwe ne ya yi kiran a ranar Laraba a Abuja a wani taron manema labarai don tunawa da taron NIQS karo na 31 da kuma babban taron cibiyar na kasa.
- Sau Ɗaya Na Taɓa Da-nasanin Fitowa A Cikin Fim – Tanimu Akawu
- Babu Wani Abu Kuskure Ga Sojan Da Ya Yi Sa-in-sa Da Ministan FCT – Matawalle
Nzekwe, wanda ya bayyana cewa, Cibiyarsa tana bai wa gwamnati shawarwari amma ya nanata cewa, alhakin gwamnati ne ta ɗauki mataki da kuma daidaita kuɗin hayar.
“Za mu ci gaba da kira ga gwamnati, da masu tsara manufofi, har ma da ‘yan majalisa, da su yi dokokin da ya dace a fannin harkokin gidaje.” In ji shi
Ya koka da cewa, ta yaya za a bayar da hayar gida mai dakuna biyu a Abuja akan naira miliyan biyar?. Dole ne a sami doka don rike hannun masu bayar da hayar gidaje.
ADVERTISEMENT














