Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa (NIS), reshen Jihar Bayelsa ta yi ƙawance da takwararta ta yaƙi da sha da safarar miyagun ƙwayoyi ta NDLEA domin tabbatar da an fatattaki masu safarar ƙwaya da baƙin-haure a jihar.
Kwanturolan reshen Jihar Beyelsa na NIS, James Sunday ya amshi baƙoncin takwaransa na hukumar yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi (NDLEA), Barista Mathew Ewa a ofishinsa da ke Yenagoa, kan wannan sabon yunƙurin nasu.
Hukumar NIS ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar 7 ga watan Satumbar 2023, wanda jami’in hulɗa da jama’a na hukumar ya rattaba wa hannu.
Sanarwar ta ce lokacin wannan ziyarar, Kwamandan NDLEA ya bayyana cewa hukumarsa za ta ƙaddamar da shirin yaƙar ta’ammuli da miyagun ƙwayoyi da kakkave baƙin haure a Jihar Bayelsa, wanda za su gudanar tare da NIS, idan Shugaban hukumar NIS, Isah Idris Jere ya amince. Haka kuma shirin zai gudana ne tare da haɗin kan Gwamnan Jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri da sauren jami’an tsaro da ke Jihar Bayelsa.
Kwamandan ya ƙara da cewa za su yi aiki kafaɗa da kafaɗa da sauran hukumomin tsaro a jihar wajen samun nasarar wannan shirin, wanda zai tsaftace jihar daga korarowar baƙin haure da masu ta’ammuli da miyagun ƙwaroyi ta hanyar bin ƙa’idogin ECOWAS idan da buƙatar hakan.
Sanarwr ta ce hukumar NIS ce za ta jagoranci shirin a wani vangare na gudanar da aiki a lokaci bayan lokaci tare da tilasta wa mazauna jihar wajen bin doka ta yadda baƙin haure ba za su karya dokokin Nijeriya da na ECOWAS na shige da fice a tsakanin mambobin ƙasashen ba.
Ta ce idan aka samu duk wani mazaunin jihar da hannu wajen gudanar da kasuwancin da ya sava da dokokin Nijeriya da na ECOWAS tare da haɗa baki da baƙin haure a lokacin wannan shirin, za a hukunta shi daidai da laifinsa kamar yadda doka ta tanada.