Hukumar Shige da Fice ta Kasa (NIS) reshen Jihar Bayelsa ta yi bikin Makon Gudanar da Bayanai da Sadarwa don kara ilmantar da Jami’an Hukumar bayanai kan ayyukan gudanarwa da hukumar a jihar a rabin farkon shekarar 2022.
A taron da ya samu halartar jami’an tsaro daban-daban da kuma masu mayar da jawabai, Gwamnan Jihar Bayelsa Sanata Douye Diri, wanda ya samu wakilcin mai ba shi shawara kan tsaro, tsohon kwamishinan ‘yan sanda mai ritaya Akpoebi Agberebi ya yi tsokaci kan nasarorin da Kwanturolar NIS Na Bayelsa, CI Sunday James ya samar cikin kankanin lokaci a jihar.
- Shugaba Buhari Ya Je Kasar Spain Ziyarar Aiki
- Sabon Rikici Ya Kunno Kai A Shugabancin Jam’iyyar APC Ta Kasa
Ya ce samar da mujallar da ke bayar da bayanan ayyukan NIS a jihar da aka a kwanan baya, ya buɗe sabon babi na adana bayanai da sanar da ayyukan hukumar a Bayelsa tare da sake bayyana rawar da NIS take takawa a harkokin tsaron jihar Bayelsa da ma kasa baki ɗaya.
Sanarwar da reshen NIS na Bayelsa ya fitar ga manema labari ta kuma fayyace muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin hukumomin da ke yaki da aikata laifuka a tsakanin dukkan jami’an tsaro a Bayelsa. Kwanturolan NIS na Jihar Bayelsa, Sunday Jame ya bayyana manufar samar da mujallar hukumar a matsayin wani kunɗi na tattara bayanan ayyuka da kuma sanar da jama’a ayyukan ci gaba na hukumar tasu.