• Leadership Hausa
Monday, March 27, 2023
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

NIS Ta Ƙaddamar Da Ba Da Sabon Fasfo A Katsina, Ta Buɗe Babban Ofishinta

by yahuzajere
2 months ago
in Labarai
0
NIS Ta Ƙaddamar Da Ba Da Sabon Fasfo A Katsina, Ta Buɗe Babban Ofishinta
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A yau Talata, Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa (NIS), ta buɗe katafaren babban ofishinta na Jihar Katsina tare da ƙaddamar da bayar da sabon ingantaccen fasfo na zamani a yankin.

Ministan cikin gida, Rauf Aregbesola ne ya buɗe ofishin tare da shugaban hukumar ta NIS, CGI Idris Isah Jere a wani ƙwarya-ƙwaryan biki da aka gudanar.

  • TARON LEADERSHIP: Buhari Ya Sauya Fasalin Tsarin Tattalin Arzikin Nijeriya —Ministan Abuja
  • Shugaban NIS Ya Sake Gargadin Marasa Gaskiya A Kan Harkokin Fasfo

Da yake jawabi a wurin, shugaban NIS, Isah Jere ya bayyana cewa, samar da sabon ingantaccen fasfo na zamani yana da matuƙar muhimmanci a cikin ayyukan da hukumar take yi wa ‘yan ƙasa, yana mai cewa, “tabbas muna sane da irin ƙalubalen da ‘yan ƙasa ke fuskanta wajen neman fasfo a lokutan baya, amma muna tabbatar muku da cewa bisa ƙoƙarin da muke yi daban-daban, kamar ƙaddamar da bayar da fasfo na zamani a Jihar Katsina, ba da jimawa ba waɗannan ƙalubalen za su kau. Muna ci gaba da ƙoƙarin buɗe ofisoshin karɓa da shigar da bayanan masu neman fasfo a jihar domin rage cunkoso. A kwanan nan za a kammala aikin ofishin na Daura tare da ƙaddamar da shi. Tuni aka samar da kayan aikin yin sabon fasfon a Katsina, nan da ‘yan kwanaki kaɗan komai zai yi daidai a fara gudanar da aiki, muna sa rai har da na Daura ma.”

NIS
NIS: Ziyarar da tawagar ta kai wa Gwamna Bello Masari a gidan gwamnatin Katsina

Isah Jere ya bayyana cewa bisa ƙaddamar da bayar da sabon fasfon na zamani, haƙiƙa za a magance tafiyar hawainiyar da ake samu wajen neman fasfo, matuƙar dai mai nema ya bi ƙa’idojin da aka shimfiɗa, ciki har da tabbatar da cewa ya gabatar da buƙatarsa ta shafin intanet tare da biyan kuɗi ta nan da kuma tabbatar da cewa bayanansa na fasfo sun yi daidai da na lambar shaidarsa ta ɗan ƙasa (NIN).

“Fasfo yana da matakai daban-daban, akwai mai aiki na tsawon shekara 10, wannan na waɗanda suka zama baligai ne da aka samar musu don magance yawan kai-komonsu a ofisoshin fasfo. Haka nan akwai sauran matakai wanda mai neman fasfo zai iya zaɓa.

Labarai Masu Nasaba

Gwamna Mai Barin Gado Da Zababbe Sun Fara Cacar Baki Kan Albashin Ma’aikata A Taraba

Abdulaziz Yari Ya Bada Tallafin Tirela 240 Na Abincin Azimi A Zamfara

“Sabon fasfon na zamani an yi shi ne da fasahar takardun zamani masu inganci wanda ruwa ba ya lalatawa, sannan yana da ƙarin alamomin tsaro guda 25 fiye da wanda ake bayarwa kafin ɓullo da shi (electronic passport). Shi wannan sabon da ake bayarwa shi ne ake yayi a halin yanzu a ɓangaren fasahar samar da fasfo a duniya, yana da ƙarko da kuma sauƙin amfani. Sannan zai yi matuƙar wahala a iya yin jabunsa saboda duk wanda ya yi yunƙurin haka ba wai kawai ba zai yiwu masa ba ne, a’a, da ya fara za a gano shi. Nijeriya ce ƙasa ta farko a duk faɗin Afirka da ta fara yin ƙaura zuwa sabon yayin na fasfo.” In ji Jere.

NIS
NIS: Minista Ogbeni Aregbesola, CGI Idris Isah Jere da wani babban jami’in tsaron fararen hula a bikin

Shugaban na NIS, ya kuma ƙara da cewa, ana ci gaba da buɗe ofisoshin bayar da sabon fasfon, har ila yau ana ci gaba da bayar da tsohon shi ma har zuwa lokacin da za a mayar da kowace cibiyar fasfo ta zama mai bayar da sabon na zamani.

Haka nan ya yi nuni da cewa, buɗe sabon katafaren ofishin NIS na Jihar Katsina, ya sake tabbatar da irin duƙufar da hukumar ta yi wajen kula da jindaɗin jami’anta. A cewarsa, “wannan zai ƙara bunƙasa ƙwazonsu su ci gaba da yin aiki tuƙuru. Ina kuma kira tare da tunatar da cewa, bisa la’akari da yanayin tattalin arzikin ƙasa, ya zama wajibi mu kula sosai da abin da muke da shi tare da yin kyakkyawan amfani da wannan sabon ginin. Wajibi ne a kula da matakan riga-kafi a kowane lokaci.”

Ya gode wa Ministan cikin gida, Ogebeni Aregbesola bisa goyon bayan da yake bai wa NIS tun daga lokacin da aka naɗa shi minista. Haka nan ya yi godiya ga shugaban ƙasa bisa rattaba hannun amincewa a takardun hukumar waɗanda suka zamo silar samun nasarorin da ake gani.

Har ila yau, shugaban na NIS, CGIS Idris Isah Jere, ya yaba da irin haɗin kan da suke samu daga sauran abokan aiki na hukumomi daban-daban da ita kanta Gwamnatin Jihar Katsina, da sarakuna da sojoji da sauransu.

  • https://leadership.ng/nis-redeploys-69-senior-officers/nigeria-immigration-service/

ShareTweetSendShare
Previous Post

Da Dumi-Dumi: Mahara Sun Kashe DPO Da Wasu A Benue

Next Post

Cikin Shekaru 3 Da Suka Gabata Sin Ta Yi Rawar Gani A Fannin Yaki Da Annobar COVID-19 

Related

Gwamna Mai Barin Gado Da Zababbe Sun Fara Cacar Baki Kan Albashin Ma’aikata A Taraba
Labarai

Gwamna Mai Barin Gado Da Zababbe Sun Fara Cacar Baki Kan Albashin Ma’aikata A Taraba

4 hours ago
Abdulaziz Yari Ya Bada Tallafin Tirela 240 Na Abincin Azimi A Zamfara
Labarai

Abdulaziz Yari Ya Bada Tallafin Tirela 240 Na Abincin Azimi A Zamfara

6 hours ago
2023: INEC Ta Sanar Da Ranar Mika Wa Zababbun Gwamnoni Takardar Shaidar Lashe Zabe
Labarai

2023: INEC Ta Sanar Da Ranar Mika Wa Zababbun Gwamnoni Takardar Shaidar Lashe Zabe

8 hours ago
SERAP Ta Nemi INEC Ta Hukunta Gwamnoni Kan Bangar Siyasa
Labarai

SERAP Ta Nemi INEC Ta Hukunta Gwamnoni Kan Bangar Siyasa

9 hours ago
DSS Ta Cafke Tsohon Soja Da Lauya Da Wasu Kan Zargin Ta’addanci
Labarai

DSS Ta Cafke Tsohon Soja Da Lauya Da Wasu Kan Zargin Ta’addanci

10 hours ago
PDP Ta Dakatar Da Tsofaffin Ministoci 2 Da Wasu 5 Kan Yi Wa Jam’iyyar Zagon-Kasa
Labarai

PDP Ta Dakatar Da Shugabanta Na Kasa Kan Zargin Yi Wa Jam’iyyar Adawa Aiki

19 hours ago
Next Post
Cikin Shekaru 3 Da Suka Gabata Sin Ta Yi Rawar Gani A Fannin Yaki Da Annobar COVID-19 

Cikin Shekaru 3 Da Suka Gabata Sin Ta Yi Rawar Gani A Fannin Yaki Da Annobar COVID-19 

LABARAI MASU NASABA

Kafar CGTN Ta Gabatar Da Jerin Bidiyo Don Yin Bayani Game Da Tsarin Demokuradiyyar Kasar Sin

Kafar CGTN Ta Gabatar Da Jerin Bidiyo Don Yin Bayani Game Da Tsarin Demokuradiyyar Kasar Sin

March 27, 2023
Kafa Dangantakar Diflomasiyya Tsakanin Sin Da Honduras Ya Sake Tabbatar Da Manufar Sin Daya Tak A Duniya

Kafa Dangantakar Diflomasiyya Tsakanin Sin Da Honduras Ya Sake Tabbatar Da Manufar Sin Daya Tak A Duniya

March 27, 2023
Gwamna Mai Barin Gado Da Zababbe Sun Fara Cacar Baki Kan Albashin Ma’aikata A Taraba

Gwamna Mai Barin Gado Da Zababbe Sun Fara Cacar Baki Kan Albashin Ma’aikata A Taraba

March 27, 2023
Abdulaziz Yari Ya Bada Tallafin Tirela 240 Na Abincin Azimi A Zamfara

Abdulaziz Yari Ya Bada Tallafin Tirela 240 Na Abincin Azimi A Zamfara

March 27, 2023
2023: INEC Ta Sanar Da Ranar Mika Wa Zababbun Gwamnoni Takardar Shaidar Lashe Zabe

2023: INEC Ta Sanar Da Ranar Mika Wa Zababbun Gwamnoni Takardar Shaidar Lashe Zabe

March 27, 2023
SERAP Ta Nemi INEC Ta Hukunta Gwamnoni Kan Bangar Siyasa

SERAP Ta Nemi INEC Ta Hukunta Gwamnoni Kan Bangar Siyasa

March 27, 2023
DSS Ta Cafke Tsohon Soja Da Lauya Da Wasu Kan Zargin Ta’addanci

DSS Ta Cafke Tsohon Soja Da Lauya Da Wasu Kan Zargin Ta’addanci

March 27, 2023
Ramadan: Lokutan Sahur Da Buda-baki Na Azumi Na 3 A Wasu Birane

Ramadan: Lokutan Sahur Da Buda-baki Na Azumi Na 5

March 27, 2023
PDP Ta Dakatar Da Tsofaffin Ministoci 2 Da Wasu 5 Kan Yi Wa Jam’iyyar Zagon-Kasa

PDP Ta Dakatar Da Shugabanta Na Kasa Kan Zargin Yi Wa Jam’iyyar Adawa Aiki

March 26, 2023
Amurka Ta Sake Zargin Kasar Sin Kan Asalin Kwayar Cutar COVID-19 Domin Yunkurin Siyasa

Amurka Ta Sake Zargin Kasar Sin Kan Asalin Kwayar Cutar COVID-19 Domin Yunkurin Siyasa

March 26, 2023
ADVERTISEMENT
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.