Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa, NIS, ta dora alhakin karancin takardun fasfo na kasa-da-kasa a kan sabon tsarin manufofin babban bankin Nijeriya, CBN.
Kwanturolan hukumar, Idris Jere ne ya bayyana haka a wani taron jin ra’ayin jama’a da wani kwamitin wucin gadi na majalisar wakilai ya shirya a Abuja.
“Tsarin siye da sayarwa na kasashen waje da kuma kin amincewar CBN na ba da damar shigo da takardun fasfo din ne ya jawo karancin takardun buga fasfo din”. Inji Jere
Ya ce umarnin da shugaban kasa ya bayar na fara samar da fasfo a cikin gida da Hukumar Buga takardu za ta fara NSPM, wannan abin farin ciki ne amma ya kamata a fara tanadar da wani shiri da zai samar da takardun kafin a fara rabuwa daga inda aka saba buga takardun.