Hukumar Kula Da Shige Da Fice ta ƙasa (NIS) ta ayyana cewa jami’anta sun cafke wasu mutane da ake zargin dillalan makamai ne a kan iyakar a Mfum da ke kan iyakar Nijeriya da Kamaru.
Garin Mfum wanda yake ƙaramar hukumar Ikom a Jihar Kuros Riba ya kasance cibiyar kasuwanci da ‘yan kasuwa na duniya ke yada zango yayin da suke safarar kayan abinci , man fetur da sauransu ta motoci zuwa ƙasar Kamaru .
Kwanturolan NIS mai kula da iyakar ƙasa ta Mfum, CI Ndubuisi Eneregbu ya yi bayanin cafke mutanen a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a ranar Lahadi .
Eneregbu ya bayyana cewa mutum uku da aka cafke sun haɗa da ‘Yan Nijeriya biyu da kuma wani baƙon-haure ɗan Kamaru wanda ya amsa cewa shi mamba ne na ƙungiyar ‘yan aware ta Ambazonia. An dai cafke su ne a kan babura ɗauke da bindigogi da albarusai .
“An cafke mutanen da ake zargin ne ɗauke da wata jaka da aka sa ƙananan bindigogi biyu da albarusai guda uku da wasu kayan tsafi da kuma waya ƙirar TECNO.
“An miƙa mutanen da makaman da aka cafke su da su ga ofishin ‘yansanda na yankin Etung domin ci gaba da bincike.
Dangane da ƙoƙarin da NIS take yi na tsaurara tsaron iyakokin ƙasa kuwa, Kwanturolan ya ce hukumar ta ƙirƙiro da gudanar da taro a kai a kai tare da sarakunan dukkan garuruwan da ke kan iyaka domin samun nasara.
“Muna da kyakkyawar alaƙa a tsakaninmu da al’ummomin da ke iyakokin ƙasa . Mun gudanar da tarurruka daban-daban da al’ummomin tare da sauran humomin tsaro. A lokacin da na kama aiki a nan yankin , abin da na fara yi shi ne ziyarar dukkan sarakunan yankunan da ke ƙarƙashin kulawar ofishinmu.
“Abin da ya sa muka yi haka kuwa shi ne mun fahimci cewa akwai buƙatar kyautata alaƙa a tsakanin jami’an tsaro da al’ummomi. Babu wata hukumar tsaro da za ta bugi ƙirji ta ce za ta iya yaƙi da matsalar tsaro ita kaɗai ba tare da goyon bayan al’umma ba.
“A shirye muke mu tabbatar da tsaro a kan iyaka tare da tsaftace ta daga masu yin zangon ƙasa ga tattalin arziki. Idan ka leƙa Mbok ko Yahe da sauran garuruwa na iyaka duk za ka tarar da jami’anmu a wurin” ya bayyana.
Tuni dai Shugaban NIS , CGI Isah Idris Jere ya yaba wa jami’an da suka yi nasarar cafke mutanen kana ya hore su su ƙara azama domin tabbatar da sauke nauyin da ƙasa ta ɗora musu.