A bisa kokarinta na kara inganta ayyukan ta, hukumar kula da shige da fice ta kasa NIS, ta bayyana cewa, ta samar da fasfo sama da miliyan 1.8 A 2022, abin da ya ninka wanda ta samar a 2021.
Shugaban hukumar na kasa, CGI Isah Jere Idris MFR ya bayyana hakan a garin Daura da ke a cikin jihar Katsina a lokacin bude ofishin fasfo a garin na Daura ranar Laraba.
Jere ya bayyana cewa, bude ofishin Fasfo na Daura, ya kara tabbatar da kokarin mahukuntan hukumar na saita hukumar don ta kai mataki irin na duniya wajen gudanar da ayyukanta.
Jere wanda ya sanar da hakan a cikin jawabinsa ya ce, ba tare da wata tantama ba, kaddamar da ofishin da kuma sauran makamancinsa da hukumar ta aiwatar, ya nuna a zahiri irin kokarin hukumar na sauke nauyin da aka dora mata na samar da fasfo ta internet don ya kai ga daukacin al’ummar kasar nan.
Shugaban ya ci gaba da cewa, bayar da fasfo din ta hanyar internet ga hakikanin ‘yan Nijeriya, na daya daga cikin nauyin da ke a kan hukumar wanda sashi na biyu na dokar hukumar ta shekara 2015 da aka sabunta ya dora mata.
A cewarsa, shekaru da dama da suka gabata, an samu gagarumin ci gaba wajen sauye -sauyen samar da fasfo daga tsohon tsari zuwa na zamani, inda ya ce, a yanzu an sabunta tsarin zuwa na internet.
Jere ya yi nuni da cewa, a yanzu ana kara samun bukatar fasfo a kasar nan, inda ya ce, a saboda hakan ne, hukumar hukumar ta kara mayar da hankali don ta cimma wannan kalubalen.
Ya ci gaba da cewa, a shekarar da ta wuce kawai, hukumar ta samar da fasfo miliyan 1.8, wanda ya rubanya wanda ta bayar har sau biyu a 2021.
Shugaban ya ci gaba da cewa, ana kuma ci gaba da yin kokari, don a bude wasu ofisoshi na fasfo a daukacin fadin Nijeriya don a rage cunkoson da ake samu na samar da fasfo a kasar nan, inda ya ce, a ranar Litinin an kaddamar da ofishin samar da fasfo a Ilesha.
Ya bayyana cewa, na garin Daura da aka kaddamar, ya bi sahun na Alimosho da ke a cikin jihar Lagos, inda ya sanar da cewa, na garin Zariya da ke a cikin jihar Kaduna da na Ilesha da ke a jihar Ogun, an bude su a wajen manyan birane ne na jihohinsu.
Ya ci gaba da cewa, don a tabbatar da an tantance bayanan masu buqatar fasfo, an hada bayanan na su da shedar katin dan kasa ta NIN.
Ya ce, inganta samar da fasfo ta internet ya zo ta fannoni da dama wanda ya hada da, na tsawon shekara goma, inda ya ce, bisa ga wannan takardun, masu buqatar fasfo a yanzu za su iya yin amfani da tsarin da suke bukata na mallakar fasfo ta internet.
A cewarsa, Nijeriya ce ta farko a Nahiyar Afrika da ta juya zuwa ga irin wannan tsarin na samar da fasfo ta internet, inda ya shawarci masu bukatar fasfo da su juya zuwa ga irin wannan tsarin na neman fasfo don bukata da kuma biyan kudin su ta shafin internet na hukumar: .immigration.gov.ng) da suke bukata.
Ya yaba wa gwamnatin tarayya kan amincawa da aikin na samar da fasfo ta internet wanda ya ke daga cikin yin amfani da fasahar zamani a iyakokin kasar nan, inda ya ce, bisa goyon bayan ‘yan hadaka an samun damar yin aiki akan lokaci na samun bayanan masu shigowa cikin kasar nan.
Ya kara da yin godiya ce, a madadin ma’aikatan hukumar, yana mai cewa, “musamman muna gode wa ministan kula da harkokin cikin gida Rauf Aregbesola, bisa goyon bayan da ya ke ci gaba da ba mu da kuma irin gudunmawar da sauran masu ruwa da tsaki har da gudunmawar da gwamnatocin jihohi da sarakunan gargajiya ke bamu.”
CGI Jere ya ba da tabbacin hukumar ta NIS za ta ci gaba da bunkasa dukkan ayyukan da tsarin mulkin kasa ya dora mata bilhakki tare da kyautata mu’amala da abokan hulda.