Mukaddashiyar hukumar kula da shige da fice ta kasa, Caroline Adepoju, ta gargadi iyaye da ‘ya’ya mata kan yin balaguro ta haramtacciyar tafiya, wanda ta ce, hakan ya janyo mutuwar wasu matsan kasar nan da dama.
Caroline ta yi wannan gargadin ne a taron ‘ya’ya mata na watan Agusta karo na 20 da ya gudana a garin Ibadan da ke a jihar Oyo.
- NIS Ta Samar Da Fasfo 38,613 Cikin Wata 5 A Ribas
- Rufe Boda: Mukaddashiyar Shugabar NIS Ta Ziyarci Iyakar Nijeriya Da Nijar Da Ke Illela
Taron mai taken ” Al’adun mabiya addinin Kirista” sashen mata na Cocin Vine ne ya shirya shi.
Shugabar ta yi nuni da cewa, masu yin irin wannan haramtacciyar tafiyar na jefa rayuwarsu a cikin hadari da cin karo da namun daji da za su iya cenye su ko kuma matsafan da za su cire wasu sassan jikinsu domin su sayar.
Kazalika, Caroline ta ja kunnen Iyayen da su kare ‘ya’yansu daga masu mayaudara ‘ma su son su fitar da su kasar waje da sunan nema masu aikin yi.
A cewarta, kimanin ‘yan Nijeriya 1,200 da ke ficewa daga kasar nan ta haramtacciyar hanya da suka mutu.
Shugabaar ta kuma shawarci ‘yan matan da su mayar da hankali wajen karatunsu tare da sa tsoron tsoron Allah a zukatansu da yin biyayya ga iyayensu.