Kungiyar Kwadago a Nijeriya NLC da takwararta ta TUC, a ranar Talata za su tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani, don nuna rashin amincewa da gazawar gwamnatin tarayya wajen aiwatar da matakan masu kyau bayan cire tallafin man fetur.
Yajin aikin da ake sa ran zai fara da tsakar daren ranar Talata 3,ga watan Oktoba, 2023.
- Yajin Aiki: Tsugune Ba Ta Kare Ba Tsakanin NLC Da Gwamnati
- Karku Kasa Barci Kan Barazanar NLC Na Tsunduma Yajin Aikin Sai Baba-ta-gani – Lalong
Da Yuyuwar yajin aikin zai gurgunta duk wasu harkokin tattalin arziki a fadin kasar sakamakon umarnin na kungiyar Kwadago na ma’aikata su kauracewa wajen ayyukansu.
A wani taron hadin guiwa da ‘yan kungiyar ta NLC da TUC suka gabatar na gaggawa da majalisar zartarwa ta kasa (NEC), sun zargi gwamnatin tarayya da gazawa wajen samar da ci gaba mai ma’ana kan batutuwan da suka dabaibaye Nijeriya bayan cire tallafin Fetur.
Kungiyoyin sun bayyana gwamnatin tarayya da rashin tabuka komai kan magance matsalolin da kungiyar kwadagon suka gabatar mata da su.