Wasu gidajen man fetur na Kamfanin Mai na kasa NNPCL sun sauya farashin man fetur zuwa Naira 860 kan kowace lita.
Duk da cewa, babu wata sanarwa a hukumance daga Kamfanin NNPCL Retail ya fitar zuwa yanzu, amma wasu gidajen man a Legas sun sauya farashin litarsu zuwa Naira 860 kan kowace lita, daga Naira 945 a ranar Lahadi.
- CMG Zai Watsa Bikin Bude Zama Na Uku Na Majalisar CPPCC Karo Na 14
- Natasha-Akpabio: Ƙungiyar Mata Ta Nijeriya Ta Gabatar Da Buƙatu Huɗu
Wannan dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan da matatar man Dangote ta rage farashin mai daga naira 890 zuwa naira 825 kan kowacce lita.
Mai magana da yawun kamfanin na NNPC, Olufemi Soneye, bai amsa kira ko sako ba game da wannan batun.
Sai dai, mataimakin shugaban kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Nijeriya (IPMAN), Hammed Fashola, ya tabbatarwa da jaridar PUNCH Online, sauya farashin litar da NNPCL ya yi a Legas.
“Gaskiya ne, NNPC na sayar da man fetur a kan Naira 860 a gidajen mai. Duk da cewa, Kamfanin bai tabbatar da hakan ba, amma sun gaya min cewa, suna aiki don fitar da sanarwar a hukumance,” in ji IPMAN.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp