Jam’iyyar NNPP ta kai korafinta ga hukumar kula da harkokin shari’a ta Nijeriya (NJC) kan kalaman rashin dacewa da mai shari’a Benson Anya ya yi kan jam’iyyar da mambobinta a lokacin kotun ta Kano ke yanke hukunci kan karar zaben gwamnan Kano.
Mai shari’a Anya ya yi zargin cewa, “A maimakon a bar wasu ‘yan siyasar a Kano su yi amfani da ‘yan fashin Siyasa da tashe-tashen hankula wajen kawar da dimokuradiyya a Jihar Kano, za a yi amfani da adalci wajen hana su ruguza dimokaradiyya a Kano zuwa sama.”
- DA DUMI-DUMI: Kotu Ta Kori Gwamna Abba Gida-Gida Ta Tabbatar Da Nasarar Gawuna
- NNPP Na Zargin Kwankwaso Da Hannu Wajen Nasarar Gawuna Da Kwace Zaben Kano A Kotu
Jam’iyyar NNPP ta sha kaye a kotun sauraron kararrakin zaben gwamna a karar da jam’iyyar APC ta shigar.
Da yake zantawa da manema labarai a Kano, shugaban jam’iyyar na jihar, Hashimu Dungurawa, ya ce a bayyane yake cewa ba a yi wa jam’iyyar adalci ba.
A cewarsa, jam’iyyar ta kai korafinta NJC akan kalaman alkalin.
“Hakika, wadannan kalamai na batanci, da kuma la’antar da aka yi mana, musamman ma kalaman mai shari’a Benson Anya ya wuce ka’idoji da tanadin shari’a” in ji shi.