Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kano (KANSEIC) ta bayyana NNPP a matsayin jam’iyyar da ta lashe zaben daukacin kujerun KaKananaHukumomin Jihar Kano 44 tare da Kansiloli 484.
Shugaban Hukumar Zaben Jihar Kano, Farfesa Sani Lawal Malumfashi ne ya sanar da haka a shelkwatar hukumar da ke Kano da yammacin ranar Asabar din nan.
Ya ce “Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kano (KANSEIC) ta aiwatar da aikin da aka dora mata, na tsarawa, shiryawa, sa ido da kuma aiwatar da zaben kanannan hukumomin Jihar Kano a tarayyar Nijeriya.
“Aikin zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali tare da samun nasarar aiwatar da shi, hukumar zaben tana bayyana matukar farin cikinta bisa gudunmawar masu ruwa da tsaki musamman jami’an tsaro, kafafen yada labarai, shuwagabanni jam’iyyu, kungiyoyin sa kai, shugabannin addini, shuwagabannin jama’a, matasa da kungiyoyin mata wajen tabbatar da cin nasarar dorewar dimokuradiyya a Jihar Kano.
“Haka kuma hukumar tana mika godiyarta ga mutanen Kano bisa hadin kai, goyon baya, addu’o’i tare da jajircewar da suka nana alokacin wannan zabe.
“Yadda zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali shi ke tabbatar da amincewar da al’umma tare da gamsuwa da tsare-tsaren hukumar ta fuskar inganci, gaskiya da mutuntuka.”
Jam’iyyu shida suka shiga wannan zabe wadanda suka hada da AA, AAC, ACCORD, ADC, APM da kuma NNPP.