• English
  • Business News
Saturday, October 25, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

NPA Ta Tarbi Babban Jirgin ‘Ruwa MB Ocean Dragon’ Don Bunkasa Ayyukanta

by Bello Hamza
4 months ago
NPA

A bisa kokarinta na kara ci gaba da amfana da hada-hadar kasuwanci a nahiyar Afika, a ranar 2 ga watan Julin 2025 ne, Hukukar Kula da Jiragen Kasa NPA, da sa’io 5:05, ta tarbi Jirgi na farko mai mai suna MB Ocean Dragon.

Jirgin wanda ya kasance yana yin zirga-jirga na kasa da kasa ne mai lamba number 9508770 an yi masa lakabi da MB Ocean Dragon, wanda kuma ya kasance, mallakin kamfanin Clarion Shipping West Africa.

  • Ƴan Bindiga Sun Yi Wa Jami’an NSCDC Ƙwantan Ɓauna A Binuwe
  • Majalisar Ta Kwace Shugabacin Kwamitin Da Natasha Ke Jagoranta

Kazalika, karfinsa ya kai 349 wanda kuma zurfinsa ya kai kafa 20 wanda kuma zai kara bunkasa zuba hannun jari.

Hakazalika, Jirgin zai kuma za a rinka yin amfani da shi, wajen gudanar da zirga-zirgar hada-hadar kasuwanci a hanyoyin ruwa a tsakanin Nijeriya da Afirka ta yamma.

Jirgin zai kuma samar da saukin jin jigilar kaya a kan hanyoyi, duba da cewa, hakan na daga cikin kokarin da NPA ke ci gaba da yi, na kara zamanantar da zirga-zirgar a Tashoshin Jiragen ruwa na kasar.

LABARAI MASU NASABA

Gwarzon Kamfanin Fasahar Kuɗaɗe Na Shekarar 2025, Opay Nigeria

Gwarzon Kamfanin Samar Da Kaya Na Shekarar 2025, Kamfanin Nestlé Pure Life

An tsara Jirgin zai rinka yin zirga-zirga ne, zuwa daukacin kasashen da ke Afirka ta yamma da kuma sama da haka, musamman yin zirga-zirga daga Nijeriya zuwa kasashen, Jamhiriyar Benin, Togo, Ghana, Kamaru, Sierra Leone, Ibory Coast, Masar, Afirka ta Kudu da sauransu, tare da kuma nuna bukatar yin kasuwanci wadda tuni, aka fara ta.

A martaninsa kan wannan nasarar, Shugaban Hukumar ta NPA Dakta Abubakar Dantsoho ya bayyana cewa, “ Wannan nasarar ta nuna irin mayar da hankalin da NPA ke ci gaba da yin a kara bunkasa ayyukan Hukumar wanda ta zo daidai da ta irin ma’aikatar bunkasa tattalin arzikin kasa.

A na ta bayanain Mataimakiyar Shugabar kamfanin na On her Clarion Shipping West Africa Limited, Bernadine Eloka, ta bayyana cewa, jigilar kaya a cikin Jirgin a Tekunan ruwan Nijeriya da kuma kokarin kara karfafa hada-hadar kasuwanci a Afrika ta yamma, za ta taimaka matuka wajen kara habaka kasuwanci.

Ta ce, manufar kamfanin shi ne, ya kara samar da saukin yin hada-hadar zirga-zigar kaya a tsakanin kasashen Afirka, musamman ta hanyar bude sabon babin kasuwanci a Tashoshin Jirgan Ruwa na Nijeriya da kasashen, Ghana, Ibory Coast da kuma sama da haka.

“Mun samar da Jirgin na MB Ocean Dragon ne, domin mu samar da saukin ga yin jigilar Kwantainoni, mai makaon yin jigilarsu, a kan tituna,” Inji ta.

Ta ci gaba da cewa, mai makon a rinka shan wahala wajen yin jigilar Kwantainoni a cikin manyan motoci daga Tashar Jirgin Ruwa ta Lekki zuwa ta Onitsha, Fatakwal, ko kuma Kalaba, Jirgin na Dragon, zai iya dakon Kwantainonin da suka kai yawan 349 ya kuma kaisu, Tashar Jirgin Ruwan da ka tsara za a kaisu, a cikin kwana biyu.

A cewarta, wannan Jirgin zai kuma taimaka wajen kara karfin guiwar sauran masu zuba hannun jari a fanin, samar da ayyukan yi da kuma rage dogaro kan Jiragen Ruwa na ketare.

Shi kuwa Manajin Darakta na mai kula da sashen kaya na kamanin Mustafa Mohammed, ya bayyana cewa, kamfanin ya mayar da hankali wajen yin gasa da sauran manyan kamfanonin kasashen duniya kamar su, Maersk Line da MSC, wanda hakan ya sanya, kamfanin ya fara turo Jirginsa na MB Ocean Dragon, zuwa cikin Nijeriya, musamman domin ya zuba hannun jarinsa a fannin sufurin Jiragen ruwan kasar.

Ya ci gaba da cewa, tuni kamfanin ya samu wasu kamfanoni da ke bukatar a yi masu dakon Kwantainoni guda 1,300, musamman wasu manoma da ke son ayi masu jigilar amfanin gona da kuma wasu masana’antu da ke bukatar a yi masu jigilar kayan da suka sarrafa, domin kar su su samu jinkirib, da zai haifar masu da yin asarar kayansu.

Kazalika, wannan ci gaban dai, na zuwa ne, daidai da sanarwar da Shugaban NPA Dakta Abubakar Dantsoho ya yi, na zuba dala miliyan 60 a matsayin sabon hannun jari, domin a kara samar da huddar cinikayya, ta kara bunkasa harkokin kasuwanci a Tashoshin Jiragen ruwa na kasar.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwarzon Kamfanin Fasahar Kuɗaɗe Na Shekarar 2025, Opay Nigeria
Tattalin Arziki

Gwarzon Kamfanin Fasahar Kuɗaɗe Na Shekarar 2025, Opay Nigeria

October 25, 2025
Tattalin Arziki

Gwarzon Kamfanin Samar Da Kaya Na Shekarar 2025, Kamfanin Nestlé Pure Life

October 25, 2025
Tinubu Ya Amince A Fara Aikin Tashoshin Jiragen Ruwa Na Apapa Da Kalaba Da Fatakwal Da Warri — NPA
Tattalin Arziki

Tinubu Ya Amince A Fara Aikin Tashoshin Jiragen Ruwa Na Apapa Da Kalaba Da Fatakwal Da Warri — NPA

October 17, 2025
Next Post
Shirin Sabunta Fata Na Tinubu Yana Samar da Damarmakin Cigaba — Minista

Shirin Sabunta Fata Na Tinubu Yana Samar da Damarmakin Cigaba — Minista

LABARAI MASU NASABA

Nafisa Abdullahi Aminu: Yarinyar Da Ta Ɗaukaka Darajar Nijeriya A Idon Duniya

October 25, 2025
Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

October 25, 2025

Bankin Providus

October 25, 2025
Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

October 25, 2025

Hukumar NASENI

October 25, 2025
An Gudanar Da Taron Cika Shekaru 80 Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan Da Dawo Da Shi Kasar Sin A Beijing

An Gudanar Da Taron Cika Shekaru 80 Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan Da Dawo Da Shi Kasar Sin A Beijing

October 25, 2025

Daɓid Adeyemi

October 25, 2025
Wakilin Sin: Shawarar GGI Ta Nuna Yadda Za A Jagoranci Bunkasa Makomar MDD

Wakilin Sin: Shawarar GGI Ta Nuna Yadda Za A Jagoranci Bunkasa Makomar MDD

October 25, 2025
Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka

October 25, 2025
Kasar Sin Ta Tsara Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-biyar Na 15

Kasar Sin Ta Tsara Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-biyar Na 15

October 25, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.