Shugaban Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa na kasa NPA, Dakta Abubakar Dantsoho ya bayyana cewa, Hukumat ta mayar da hankali, wajen inganta rayuwar ma’aikatanta.
Dantsoho ya kara da cewa, hakan na kuma daga cikin dabarun da ke kara masu kwarin guiwar, gudanar da ayyukansu.
- Ƴan Bindiga Sun Yi Wa Jami’an NSCDC Ƙwantan Ɓauna A Binuwe
- An Bude Taron Ministoci Kan Wayewar Kai A Birnin Beijing
Shugaban ya bayyana cewa, a saboda wannan dalilin ne, Hukumar ta karawa ma’aikatan guda 1,500 matsayi.
Dantsoho wanda ya sanar da hakan a lokacin da kungiyar ma’aikata ta MWUN da kungiyar manyan ma’aikatan Hukumar da kuma kungiyar ma’aikatan kamfanon SSASGOC, suka yaba masa na wannan karin matsayin na ma’aikatan Hukumar.
Ya ci gaba da cewa, ta wannan hanyar ce kawai, Hukumar za su damar cimma burin da masu ruwa da tsaki suke da shi, musamman domin Hukumar ta kara tabbatar da gasa, ta hanyar karin matsayin, a tsakanin ma’aikatanta.
Dantsoho ya kara da cewa, nuna kwarewar ma’aikata na kara taimaka wa, wajen cimma burin da aka sanya a gaba, musamman a bangaren nuna yin gasa, a tafiyar da Tashohin Jiragen Ruwa.
“Ta irin wannan hanyar ce, za mu iya cimma bukatar da muke da ita da kuma cika muradin masu ruwa da tsaki, da ke a fannin, musamman domin mu kara karfafa karsashin ma’aikatan mu,” Inji Dantsoho.
Dantsoho ya kuma jinjinawa Minsitan ma’aikatar bunsa hada –hadar kasuwanci na kan Teku Adegboyega Oyetola, kan sahalewar Hukumar ta NPA, na yin karin girman ga ma’aikatan da suka amfana, wanda Hukumar ta jima, tana da bukatar yin hakan.
“Dole ne kuma in yabawa Ministanmu Adegboyega Oyetola, kan amincewar da ya yi, na kawo karshen batun yiwa ma’aikatan karin matsayin, ta hanyar gudanar masu da jarrabawar yin gwaji,” A cewar Shugaban.
A na sa jawabin madadin gamayyar kungiyoyin na Tashoshin Jiragen Ruwan kasar SSASCGOC, Kwamarade Bodunde, ya nuna jin dadinsa kan wannan karin matsayin da aka yiwa ma’aikatan.
“Muna kuma godiya, kan inganta walwalar ma’aikatan Hukumar ta NPA da kara inganta ayyukan ‘ya’yan kungiyar, musamman duba da irin yanayin matsin tattalin arzikin da ake fama da ita a kasar, Inji Bodunde.”
Shi kuwa, Janar Manaja a sashen tsare-tsare da samar da bayanai na Hukumar ta NPA Ikechukwu Onyemekara, ya bayyana cewa, zamanantar da kayan aikin Tashoshin Jiragen Ruwan kasar, hakan zai kara taimaka wa wajen kara inganta ayyukan ma’aikatan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp