• English
  • Business News
Thursday, October 16, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

NRC Ta Dakatar Ma’aikacinta Kan Karbar Kudin Fasinja Ba Bisa Ka’ida Ba

by Abubakar Abba
2 years ago
NRC

Biyo bayan zargin da ake yi wa wasu daga cikin ma’aikatan hukumar kula da sufurin jiragen kasa (NRC), da suke aiki a tashar jirgin kasa ta Obafemi Awolowo na kyale fasinjoji hawan jirgin kasa daga jihar Legas zuwa Ibadan ba tare da sun sayi tikiti ba, mahukuntar hukumar, sun dakatar da wani ma’aikaci da faifan bidiyo ya fallasa shi yana karbar kudin hawa jirgin daga hannun wasu fasijoji. 

Faifan bidiyon wanda ya karade shafukan sada zumunta, ya bayyana ne, ranar 2 na watan Okutobar 2023, wanda ya nuna ma’aikacin na shawartar wasu fasinjojin cewa, ba sai sun sayi tikitin kafin su hau jirgin ba, amma ya daidaita da su yayin da suka shiga cikin jirgin.

  • Ambaliyar Ruwa Ta Raba Mutane 563 Da Muhallansu A Adamawa
  • Gajiya Ce Ta Sa Na Fadi Yayin Tantance Ni A Majalisa — Balarabe

Kazalika, sama da fasinjoji 60 ne aka yi zargin cewa, ko wannensu, ya biya kudi Naira 3,600 kafin su shiga jirgin daga tashar Obafemi Awolowo.

A cikin wata sanarwa da mataimakin mai hulda da jama’a na hukumar, Mista Yakub Mahmood, ya rattabawa hannu ta ce, an dakatar da ma’aikacin har sai kwamitin bincike, ya gabatar da rahotonsa a kan zargin.

Yakub, ya danganta laifin da ake zargin ma’aikacin a matsayin saba wa dokoki da ka’idar da hukumar ta gindaya.

LABARAI MASU NASABA

Shugaban Ƙasa Zai Sake Nazari Kan Mutanen Da Aka Yi Wa Afuwa

Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara

Bugu da kari, ya shawarci fasinjoji da ke son yin tafiya a cikin jirgin kasa, da su tabbatar sun sayi tikiti kafin su shiga cikin jirgin.

Ya ce, duk wani ma’aikacin hukumar da aka kama ya na karya dokar hukumar, za a hukunta shi kamar yadda doka ta tanada.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tinubu
Manyan Labarai

Shugaban Ƙasa Zai Sake Nazari Kan Mutanen Da Aka Yi Wa Afuwa

October 16, 2025
Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara
Labarai

Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara

October 16, 2025
Sabbin Ministoci
Manyan Labarai

Majalisar Dattawa Ta Amince Da Amupitan A Matsayin Shugaban INEC

October 16, 2025
Next Post
Zan Ware 10bn Don Inganta Ilimin Matasa Idan Na Ci Zabe – Atiku

Atiku Zai Yi Jawabi Kan Shaidar Karatun Tinubu Ta Jami'ar Chicago

LABARAI MASU NASABA

Tinubu

Shugaban Ƙasa Zai Sake Nazari Kan Mutanen Da Aka Yi Wa Afuwa

October 16, 2025
Xi Jinping Ya Yi Kira Da a Kara Horar Da Kwararrun Masana A Fannin Aikin Gona

Xi Jinping Ya Yi Kira Da a Kara Horar Da Kwararrun Masana A Fannin Aikin Gona

October 16, 2025
Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara

Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara

October 16, 2025
Shugabannin Kasashe Da Dama Sun Yaba Wa Sin Kan Gudummawar Da Ta Bayar A Fannin Tabbatar Da Daidaiton Jinsi

Shugabannin Kasashe Da Dama Sun Yaba Wa Sin Kan Gudummawar Da Ta Bayar A Fannin Tabbatar Da Daidaiton Jinsi

October 16, 2025
Sabbin Ministoci

Majalisar Dattawa Ta Amince Da Amupitan A Matsayin Shugaban INEC

October 16, 2025
Ɗaga Matsayin Dangantakar Zambia Da Sin Ya Haifar Da Manyan Nasarori

Ɗaga Matsayin Dangantakar Zambia Da Sin Ya Haifar Da Manyan Nasarori

October 16, 2025
Gwamnatin Tarayya Za Ta Tallafa Wa Fursunoni Bayan Kammala Zaman Kurkuku

Gwamnatin Tarayya Za Ta Tallafa Wa Fursunoni Bayan Kammala Zaman Kurkuku

October 16, 2025
Amupitan Ya Isa Majalisar Dattawa Domin Tantance Shi A Matsayin Sabon Shugaban INEC

Amupitan Ya Isa Majalisar Dattawa Domin Tantance Shi A Matsayin Sabon Shugaban INEC

October 16, 2025
Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC

Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC

October 16, 2025
An Dakatar Da Tashi Da Saukar Jirage A Kenya Don Karɓar Gawar Raila Odinga

An Dakatar Da Tashi Da Saukar Jirage A Kenya Don Karɓar Gawar Raila Odinga

October 16, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.