Kwalejin Tulip Nijeriya ta kasa da kasa Yobe (NTIC) ta nuna jin dadinta dangane da gudunmawar da mai girma Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, saboda irin maida hankalinsa da yayi kan lamarin daya shafi ilimin yara manyan gobe.
Har ila yau makarantar tayi bikin murnar hazikan dalibanta, wadanda suka ci gaba da samun nasara a lamarin da ya shafi ilimi da kuma wasu abubuwan da suka sha bamban da shi a cikin gida da kuma waje.
Manajan darekta na NTIC, Dakta. Feyzullah Bilgin, yace nasarorin da aka samu sun hada da jarabawar shiga manyan makarantu ta kasa (JAMB) da sauran jarabawar daban- daban na kasa, sai kuma nasarorin da aka samu a duniya.
Ya kara da cewa daliban Kwalejin NITIC ta Yobe wani babban lamari ne da yasa ayi takama da su saboda kuwa sannu a hankali sai nasarori suke kara samu wajen wakiltar Jihar Yobe da kuma Nijeriya.
Nasarorin da ba’a dade da samun su ba sun hada da, matsayi na farko a jarabawar Lissafi da aka yi ta kasai da kuma Olympiad inda aka samu nambar gwal a gasar harshe ta duniya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp