Hukumar kula da jami’o’i ta kasa (NUC) ta daga darajar kwalejin ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke Kumbotso a jihar Kano zuwa jami’a.
Abubakar Rasheed, sakataren zartarwa na NUC, ya mika takardar amincewa ta hukumar ga gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje a Abuja a ranar Talata.
Rasheed ya ce, Jami’ar Sa’adatu Rimi ta kasance jami’a ta 61 mallakar gwamnatin jihohi kuma jami’a ta 221 da ke fadin Nijeriya.
“Bayan cika sharuddan da ake bukata, na rubuta a madadin hukumar NUC cewa, daga ranar Talata 14 ga Fabrairu, 2023, Jami’ar Ilimi ta Sa’adatu Rimi ta zama jami’a ta 61 mallakin jihohi kuma jami’ar ta 221 a Nijeriya,” inji shi.
“Akan wannan takardar karin girma, an sanar da Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami’a (JAMB) da Asusun Tallafawa manyan makarantu (TETFund) da Hukumar Kula da matasa ‘yan hidimar kasa (NYSC) game da wannan sabuwar jami’ar.”
A nasa jawabin, Ganduje ya ce, wannan nasara, ta mayar da jihar Kano ta mallaki Jami’o’i mallakin gwamnatin jihar guda Uku.
Sauran biyun, sune: Jami’ar Yusuf Maitama Sule da Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil.