Kwanan baya, Amurka ta tilastawa abokan cinikinta da su mika wuya ta hanyar shawarwari da ita kan batun harajin kwastam. A cikin shawarwarin da Japan, Amurka ta nemi Japan da ta nuna sassauci kan darajar kudin musanyar kasashen biyu, da kara kudaden tsaro da sauransu, daidai da abubuwan da suka dace da moriyar Amurka kadai.
Babu kasashe ko yankuna da dama da suka aminci da sakon da Amurka ke fitarwa, wato yin shawarwari bisa harajin. Dalilin da ya sa hakan shi ne, matakin harajin da Amurka ke dauka tamkar sakon tayar da yaki tsakaninta da duk fadin duniya ne. Kasashe da dama na ganin cewa, nuna sassauci ko mika wuya ba zai kawo zaman lafiya ba ko kadan, kuma ba za a mutunta kasa dake yin hakan ba.
Ban da wannan kuma, kasuwar hada-hadar kudin Amurka ta girgiza a kwanan baya, inda al’ummun Amurka suka nuna matukar damuwa kan koman bayan tattalin arziki, kana yawan goyon bayan da shugabannin kasar ke samu ta fuskar tattalin arziki ya ragu zuwa matsayi mafi kankanta a tarihi. Hakan ya bayyana cewa, bangaren siyasa, da tattalin arziki, da sauran bangarori suna kayyade mummunan matakin ciniki da gwamnatin ke dauka. A bangaren kawayenta dake da dankon zumunci tsakaninsu na dogon lokaci kuwa, sun bayyana rashin jin dadinsu duba da matakin babakere a bangaren cinikin da ta dauka. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp