Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a zaben 2023 Dr. Peter Obi, ya yi wata ganawar sirri da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Dr. Sule Lamido.
Sai dai ba a bayyana dalilan ganawar tasu ba, Mai taimaka wa Dakta Sule Lamido a kafafen yada labarai na zamani, Mansur Ahmed, ya bayyana cewa ganawar ta dauki akalla tsawon awanni 2 suna tattaunawa a gidan na Alh. Sule Lamido.
Tun bayan zaben shekarar 2023 an hango Peter Obi na kai ziyara a wurin manyan ‘yan siyasa da halartar taruka a jihohi da dama, wanda hakan ke nuna alamun yana kan bakarsa na muradin sake tsayawa takarar shugaban kasa a kakar zaben 2027.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp