Bayanai na nuna cewa, a ’yan shekarun baya-bayan nan, ofisoshin kwastam na kasar Sin, sun samu babban ci gaba wajen sa kaimi ga gudanar da harkokin kasuwanci a kan iyakokin kasar.
Wani jami’in hukumar kwastam mai suna Zhao Zenglian, ya shaida wa taron manema labarai cewa, lokacin da hukumar ke dauka wajen tantance kayayyakin da ake shigo da fitar da su, ya ragu sosai.
Zhao ya ce a shekarar 2022, baki dayan lokacin da aka dauka wajen shigo da ma fitar da kayayyaki don kammala aikin kwastam, ya kai sa’o’i 32.02 da sa’o’i 1.03, bi da bi, raguwar kashi 67.1 da kashi 91.6 kan na shekarar 2017.
Sauran abubuwan da aka samu ci gaba, sun hada da raguwar farashi da takaita hanyoyin shigo da kaya da ma fitarwa, da nufin rage kudaden da kamfanoni ke kashewa, da kuma biyan bukatun kasuwancin su.
Taron manema labarai na ranar Talata ya kuma bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin ta yi amfani da shawarwari 148 da wakilan majalisar wakilan jama’ar kasar suka gabatar da kuma shawarwari 141 da mambobin kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama’ar kasar Sin suka bayar a bara. (Ibrahim Yaya)