Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya sanar da cewa kananan bankuna irinsu Opay, Palmpay, Kuda da Moniepoint da aka umurta su daina amsar sabbin kwastomomi a kwanakin baya, za su ci gaba da amsar kwastomomi nan da watanni biyu masu zuwa.
Gwamnan babban bankin na kasa, Olayemi Cardoso ne ya bayyana hakan a karshen taron koli na bankin karo na 295 da aka gudanar a Abuja ranar Talata.
Olayemi ya ce, babban bankin na CBN ya jawo hankalin mahukunta kananan bankunan kan bukatar inganta ayyukansu, inda ya kara da cewa, a wani yunkuri na dakile haramtacciyar hanyar hada-hadar kudade, CBN ya bullo da matakan da za su inganta tare da karfafa tsaro kan hada-hadar kudade na tsoffi da sabbin kwastomomin kananan bankunan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp