Kamfanin samar da lantarki da hasken rana a Nijeriya da kuma kamfanin kasar Azerbaijan na daga cikin kamfanoni 55 da suka amfana da tallafin dala biliyan 1.7 daga kungiyar kasashen masu fitar da man fetur OPEC a shekarar 2023.
Haka kuma shirin tallafin ya samar da Dala biliyan 25 don aikin samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana a kasar Nijar haka kuma za a ba kasar Azerbaijan Dala miliyan 50 don samar da harken lantarki mai aiki da iska mai karfin migawat 240.
- An Gama Aikin Bitar Liyafar Bikin Bazara Karo Na 5 Ta Kasar Sin
- Yadda Nijeriya Ta Taka Rawar Gani Har Zuwa Zagayen Karshe Na Gasar AFCON
Shirin samar da wutar lantarki na kungiyar OPEC zai karfafa harkar samar da wutar lantar mai amfani da harken rana a kasashen Tanzania da Bangladesh, kamar dai yadda shirin muradunm karni na 7 ya tanada na samar da tsaftaccen wutar lantarki wanda baya cutar da muhalli.
Bugu da kari an kuma samar da wasu kuadden don fuskantar matsaloli irinsu dumamar yanayi, zamantakewa da tattalin arziki.
Darakta a kungiyar, Abdulhamid Al-Khalifa, ya bayyana muhimman gudumawar da suka bayar wajen shawo kan matsalolin sauyin yanayi da dumamar yanayi da ke fuskanta duniya.
Ya kuma kara da cewa, “a shekarar 2023, OPEC ta kara yawan kudaden da take bayarwa don karafafa yaki da ake yi da matsalolin dumamar yanayi, “mun kuma fadada wadanda suke amfana da kuadden da muke bayarwa don dukkan bangarori su amfana.”
Al-Khalifa ya kuma nemi hadin kai a tsakanin kasashe da hukumominsu, “Don sai da hadin kai za a tabbatar da dukkan wadanda ake yi dominsu sun amfana” In ji shi.