Mambobin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta kasa (ASUU) a ranar Litinin sun sake zaban Farfesa Emmanuel Osodeke a matsayin shugabansu na kasa ba tare da wata hamayya ba domin ya jagoranci harkokin kungiyar na tsawon wasu shekaru biyu masu zuwa.
Kazalika, kungiyar ta kuma sake zabin Farfesa Chris Piwuna na kwalejin koyar da ilimin likitanci a jami’ar Jos, a matsayin mataimakin shugaban kungiyar na kasa.
- ASUU Ta Tsunduma Yajin Aiki A Jami’ar Taraba
- ASUU: Yadda ‘Yan Nijeriya Ke Dafifin Koma Wa Jami’o’i Masu Zaman Kansu
Jagororin sun samu wannan zarafin ne a yayin zaben kungiyar karo na 22 da ya gudana a jami’ar Jos ta jihar Filato tsakanin ranakun 19 zuwa 21 na watan Mayun 2023.
Sauran manyan mukaman da kungiyar ta sake zaba sun kunshi: Farfesa Siji Sowande a matsayin ma’aji: Farfesa Ade Adejumo aka zaba a matsayin sakataren kudi; Dakta Austen Sado (Sakatare); Drakta Adamu Babayo (Mai bin diddigin kudaden) da kuma Dakta Aisha Bawa da ta maye gurbin Dakta Stella-Maris Okey a matsayin sakataren walwala da jin dadin mambobi.
Osodeke da take jawabi bayan taron, ya misalta zaben a matsayin wanda aka gudanar bisa nagarta da kwanciyar hankali.
Ya ce za su fitar da cikakken sanarwar manema labarai kan taron nasu da kuma sake zabin nasa da sauran manyan mukaman da aka yi idan suka koma Abuja.