Sabon zababben gwamnan jihar Osun a inuwar Jam’iyyar PDP, Sanata Ademola Adeleke, ya Karyata rade-radin da ake yadawa cewa ministan kula da harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ne ya taimaka masa lashe zaben Kujerar Gwamna a jihar.
In ba a manta ba, an zabi Adeleke a matsayin sabon gwamnan jihar ne a makon da ya gabata, bayan da gwaman jihar mai ci, Gboyega Oyetola na Jam’iyyar APC ya sha kaye a hannun Adeleke.
An dai yi ta yin hasashen cewa, rashin jituwar dake tsakanin dan takarar shugaban kasa a APC, Bola Tinubu da Aregbesola ne ya janyo APC mai mulki a a jihar ta sha kasa a lokacin zaben gwamnan na jihar Osun.
Amma Adeleke a martanin da ya mayar a hirarsa da gidan talabijin na Channels ya ce sam bawata ganawa ta musamman dake tsakaninsa da Minista Aregbesola kafin gudanar da zaben a jihar.
Sai dai ya aminta da cewa wasu abokan siyasar ministan sun hada kai da shi wajen samun nasarar sa akan Oyetola.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp