Babban bankin kasar Sin (PBOC) ya sha alwashin ci gaba da sanya kudinsa ta hanya mafi dacewa wajen zuba jari da samar da kudade tsakanin kasashe.
A cikin wata sanarwa da bankin ya fitar ta shafinsa na Wechat jiya Lahadi, ya bayyana cewa, zai ci gaba da inganta darajar kudin kasar wato Yuan. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)