Jam’iyyar PDP a Jihar Sakkwato ta yi Allah-wadai da yadda hukumar EFCC ta tsare tsohon gwamnan jihar, Sanata Aminu Waziri Tambuwal.
PDP ta ce wannan mataki wani ɓangare ne na yadda gwamnatin APC ke amfani da hukumomi wajen zaluntar ‘yan adawa.
- An Rufe Kwaleji A Bauchi Bayan Zanga-zangar Ɗalibai Kan Fashi Da Makami
- Ba Iya Yunwa Ce Kaɗai Ke Kashe Ƙananan Yara A Katsina Ba – Gwamnati
Kakakin jam’iyyar a jihar, Hassan Sahabi Sanyinnawal, ya shaida wa manema labarai a safiyar ranar Talata cewa Gwamnatin Tarayya tana amfani da hukumomi don takura wa ‘yan adawa.
A cewar PDP, tsare Tambuwal wani cin zarafi ne da ake yi wa ‘yan siyasa da ke sukar abin da ta kira mulkin kama-karya na gwamnatin Tinubu.
Jam’iyyar ta ce an yi hakan ne domin ɓata masa suna da kuma hana ‘yan adawa damar yin magana.