Jam’iyyar PDP ta yi ikirarin cewa, wasu makiyan dimokardiyya ne suka yi kokarin hargiza gangamin yakin neman zaben da dan takara shugaban kasa na PDP Atiku Abubakar da aka gudanar a jiya Litinin a jihar Kaduna.
A cikin sanarwar da sakataren PDP na kasa Debo Ologunagba ya fitar a Abuja ya ce, wasu makiyan dimokuradiyya ne suka debo ‘yan bayar bangar siyasa domin su hargiza gangamin, musamman ganin cewa, ba su ji dadin kokarin da PDP take kan yi na sasanta ‘ya’yan PDP da suke ganin PDP ta saba masu.
Ya sanar da cewa, yunkurin na makiyan dimokursdiyya, ba zai karkatar da hankalinta ba wajen kokarin ta tsamo kasar daga cikin halin da ta tsinci kanta.
Ya yi kira ga jami’an tsaro da su gaggauta bankado wadanda suka turo ‘yan bangar siyasan don hargiza gangamin na PDP a Kaduna don a kaucewa kara afkuwar hakan a nan gaba.