A yayin da aka shiga jajibirin ranar yara ta duniya, Peng Liyuan, mai dakin shugaban kasar Sin Xi Jinping, da kungiyar raya masu dakin shugabannin kasashen Afirka, sun kaddamar da wani shirin hadin gwiwa, da zai taba zukatan yara marayu na kasashen Afirka. Ofisoshin jakadancin kasar Sin dake kasashen Afirka da tawagogin likitocin dake kasashen da abin ya shafa, sun ziyarci kananan yara a gidajen kula da marayu ko cibiyoyin da ke da alaka da su, inda suka gudanar da aikin duba lafiyarsu kyauta, tare da ba da gudummawar kunshin kayayyaki da dai sauransu.
A cikin shirin nata, Peng Liyuan ta bayyana fatan cewa, kula da lafiyar marayu na Afirka, zai inganta lafiya da jin dadin yaran nahiyar Afirka, da ba da gudummawa wajen gina al’ummar Sin da Afirka mai kyakkyawar makoma ta bai daya a sabon zamani.
A nata bangare, Monica Geingos, shugabar karba-karba ta kungiyar ci gaban matan shugabannin kasashen Afirka, kuma uwargidan shugaban kasar Namibiya, da mambobin kungiyar sun mayar da martani mai kyau, tare da yabawa da kulawar da Peng Liyuan ta nuna na dogon lokaci, da yadda take goyon bayan ci gaban mata da kananan yara a nahiyar Afirka. (Mai fassarawa: Ibrahim)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp