Uwargidan shugaban kasar Sin, kuma wakiliyar UNESCO ta musamman, kan inganta ilimin yara mata da mata, Peng Liyuan, ta gabatar da jawabi ta kafar bidiyo ga dandalin matan kasashen Sin da Afirka Alhamis din nan.
Yayin jawabin nata, Peng Liyuan ta bayyana cewa, Sin da Afirka sun dora muhimmanci matuka kan raya harkokin mata. Kasar Sin na kara inganta tsarin doka, da nufin kare ’yancin mata da moriyarsu, da inganta matakin ilmin mata, da tallafawa harkokin kasuwanci da kirkire-kirkire na mata, da inganta harkokin kiwon lafiyar mata da kananan yara, da samar da yanayi mai kyau na ci gaban mata.
Ta bayyana cewa, kasashen Afirka sun yi kokarin inganta yanayin da mata ke rayuwa da ma samar da kayayyaki, da taimaka musu wajen rage radadin talauci, da karfafa musu gwiwar shiga cikin harkokin kasa da na zamantakewa, kuma sun samu sakamako mai kyau.
A game da tafarkin bunkasa harkokin mata kuwa, Madam Peng ta ce, kasashen Sin da Afirka suna da buri iri daya, kuma sun kasance abokan da tafiya tare.
A yau ne dai, aka bude taron dandalin matan kasashen Sin da Afirka, wanda kungiyar mata ta kasar Sin da gwamnatin jama’ar lardin Hunan suka dauki nauyin shiryawa a birnin Changsha na lardin Hunan na kasar Sin. (Ibrahim Yaya)