Uwar gidan shugaban kasar Sin Peng Liyuan, ta gana da safiyar yau Litinin da Ngo Phuong Ly, uwar gidan To Lam, shugaban kasar Vietnam kuma babban sakataren kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta Vietnam, wadda ta rako mijinta dake ziyarar aiki a kasar Sin.
Yayin ganawar, Peng Liyuan ta ce, Sin da Vietnam makwabta ne na kwarai, haka kuma kasashen biyu na da kamanceceniya a bangaren al’adu da adabi da fasahohi da abinci da sauransu, kuma tana fatan bangarorin biyu za su karfafa musaya da hadin gwiwa da zurfafa fahimtar juna da inganta raya abotar Sin da Vietnam. A cewarta, Vietnam ta samu gagarumin ci gaba don gane da harkokin da suka shafi mata, ciki har da ilmantar da mata da ‘yan mata, tana mai cewa bangarorin biyu za su iya karfafa musaya da koyi da juna.
A nata bangare, Ngo Phuong Ly ta bayyana matukar sha’awar al’adun Sinawa tare da fatan ci gaba da inganta musayar al’adu da fahimtar juna tsakanin Sin da Vietnam. Ta ce, ya kamata bangarorin biyu su ci gaba da musaya tsakanin mata da matasa da zurfafa fahimtar juna da karfafa abota tsakanin al’ummominsu. (Fa’iza Mustapha)