Peng Liyuan, uwargidan shugaban kasar Sin Xi Jinping, ta gana ta Denise Nyakeru Tshisekedi, uwargidan shugaban Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, Felix-Antoine Tshisekedi Tshilombo, jiya Juma’a, a birnin Beijing.
Yayin ganawar, Peng Liyuan ta yaba da kokarin da Denise Nyakeru ke yi wajen inganta kiwon lafiya da walwalar mata da yara da matasa a Afrika, a matsayinta na mataimakiyar shugabar kungiyar matan shugabannin kasashen Afrika domin ci gaba (OAFLAD).
A cewar madam Peng, kasar Sin za ta ci gaba da musaya irinta abota da kungiyar OAFLAD, kuma a shirye kasar take ta karfafa hadin gwiwa tare da hada hannu da kungiyar wajen bayar da karin gudunmuwa ga inganta batutuwan da suka shafi mata da yara da kuma gina al’ummar Sin da Afrika mai makoma ta bai daya a sabon zamani.
A nata bangare, Denise Nyakeru, ta yabawa daddaden goyon baya da kulawar da Peng Liyuan ke bayarwa ga ci gaban mata da yara da matasan kasashen Afrika, kuma ta na sa ran karfafa musaya da hadin gwiwa da ma hada hannu da ita wajen ciyar da abotar Sin da Afrika gaba. (Fa’iza Mustapha)