A jiya ne, uwargidan shugaban kasar Sin Xi Jinping, Madam Peng Liyuan, ta gana da uwargidan shugaban Zambia Mutinta Hichilema, wadda ta rako shugaban na Zambia Hakainde Hichilema a ziyarar aikin da ya kawo kasar Sin.
A yayin ganawar tasu a birnin Beijing, madam Peng ta bayyana cewa, ta yaba da yadda uwargidan shugaban Zambia ta dade tana mai da hankali kan ayyukan jin kai da jin dadin jama’a, da kuma kokarin da take yi na kare hakkoki da muradun kungiyoyi masu rauni da mata da kananan yara.
Ta kuma yi karin haske kan nasarorin da kasar Sin ta cimma a fannin ba da ilmi ga mata da ‘yan mata, da aikin rigakafin cutar kanjamau, da ci gaban da kasar ta samu wajen kyautata ‘yancin nakasassu.
Peng ta bayyana cewa, kasashen Sin da Zambia na da dadaddiyar abokantaka, kuma layin dogo na Tazara, wani abin misali ne na wannan abokantaka. Ta ce ta yi imanin cewa, a bisa jagorancin shugabannin kasashen biyu, bangarorin biyu za su ci gaba da karfafa mu’amala da hadin gwiwa a fannoni daban daban, da ma samar da moriya ga jama’arsu.(Ibrahim)